Tinubu Da Atiku Ba Su Cancanci a Ayyana Su Matsayin Shugaban Kasa Ba, Shaidar Atiku Ya Fadawa Kotu

Tinubu Da Atiku Ba Su Cancanci a Ayyana Su Matsayin Shugaban Kasa Ba, Shaidar Atiku Ya Fadawa Kotu

  • Shaidar PDP ya yi wata fallasa mai ban mamaki game da muhimmancin kaso 25% na ƙuri’un FCT a lokacin zaɓen shugaban ƙasa
  • A cewar Mohammed Aliyu, kaso 25% na ƙuri’un birnin tarayya (FCT) Abuja wajibi ne wajen cin zaɓen shugaban ƙasa
  • Shaidan ya jaddada cewa furucin nasa ba ra’ayinsa ba ne, iyaka dai ya dogara ne da abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada

Abuja - Wani shaida na jam'iyyar PDP da ɗan takararta na shugabancin ƙasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya bayar da shaida da ke ƙalubalantar ɗan takarar na PDP.

Shaidan ya shaidawa kotu cewa Atiku da Bola Tinubu na jam’iyyar APC ba su cancanci a ayyana su a matsayin shugaban ƙasa ba, saboda rashin samun kaso 25% cikin 100% na ƙuri'un babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule Da Kungiyar Ma'aikata Ta Kasa Kan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

Atiku da Tinubu ba su samu kaso 25 na FCT ba
Shaidar PDP ya ce Tinubu da Atiku ba su cancanci zama shugaban kasa ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Doka ce ta tanadi hakan, dole mutum ya samu kaso 25 cikin 100 na FCT

Da yake amsa tambayoyi daga lauyan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Mohammed Aliyu, ya ce sharaɗi ne na dole mutum ya samu kaso 25% cikin 100% na kuri'un FCT kafin a bayyana shi a matsayin shugaban ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake ƙarin haske a kan hakan, ya bayyana cewa furucin nasa da ya yi ra'ayinsa ne kuma ya dogara ne da abin da doka ta zo da shi.

Da yake tabbatar da ko Atiku ya samu sakamakon da ake bukata a babban birnin tarayya ko bai samu ba, Aliyu ya ce:

"Dan takara na bai samu kaso 25% na ƙuri'un babban birnin tarayya (FCT) Abuja ba bisa ga sakamakon da INEC ta wallafa."

Kara karanta wannan

Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa

Peter Obi ya gabatar da shaidu kan nasarar Tinubu cikin akwatin zaɓe a gaban kotu

Dan takarar shugabancin ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya kai shaida a cikin akwatunan zaɓe a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a 1 ga watan Yuni.

A cikin wani faifan bidiyo na daƙiƙa 41 da jaridar The Nation ta wallafa a shafinta na Tuwita @TheNationNews, an gabatar da akwatunan ɗauke da takardun zaɓe a gaban kotu.

Sai dai kotu ta yi watsi da matakin da Obi da lauyan jam’iyyar Labour, Emeka Okpoko, suka ɗauka na yin amfani da takardun da ba a shigar ba wajen gabatar da ƙara bisa dalilin rashin bin doka da oda.

Jam'iyyun adawa sun caccaki Tinubu kan jan ƙafa wajen bayyana kadarorinsa

A wani labarin namu na baya, jam'iyyun adawa sun caccaki sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima kan jan ƙafar da suke ta yi wajen bayyana yawan kadarorinsu a gaban hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata (CCB).

Kara karanta wannan

“Gwamnati Mai Ci A Yanzu Ta Wucin Gadi Ce, Zan Karbo Kujerata a Kotu”, Atiku Abubakar

Manyan jam'iyyun adawa, wato jam'iyyar PDP da Labour Party ne dai kan gaba wajen azalzalar shugaban ƙasar kan batun bayyana kadarorin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel