Sauki Zai Zo: Oshiomole Ya Bayyana Shirin Gwamnatin Tinubu Na Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur

Sauki Zai Zo: Oshiomole Ya Bayyana Shirin Gwamnatin Tinubu Na Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur

  • Ƴan Najeriya sun shiga cikin wani hali a dalilin tsige tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi
  • Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya ce akwai shiri na musamman da gwamnatin tarayya ke yi domin rage raɗaɗin hakan
  • A cewarsa gwamnatin tarayya za ta inganta albashin ma'aikata domin ciro su daga halin da suka tsinci kansu kan cire tallafin

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana da shiri na musamman domin rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya janyo wa ƴan Najeriya.

Oshiomole ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar ta lura da matsanancin halin da aka fara shiga a dalilin cire tallafin, kuma tana yin shiri domin kawar da hakan da gaggawa, cewar rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Mutane Da Dama Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Kano

Oshiomole ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na rage radadin cire tallafin man fetur
Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne bayan gudanar da taron wakilan gwamnatin tarayya da na ƙungiyar ma'aikata ta ƙasa (TUC), akan cire tallafin man fetur ɗin.

Ya bayyana cewa shugaban ƙasa Tinubu ya lura da halin da mutane suka fara shiga kan cire tallafin, kuma yana da tsarin kawar da hakan cikin gaggawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin tarayya za ta inganta albashi

Ya bayyana cewa hanyar magance hakan da suka tattauna a lokacin taron ita ce, gwamnatin za ta inganta yanayin albashi domin rage raɗaɗin tsadar rayuwar da aka shiga, rahoton Punch ya tabbatar.

A kalamansa:

"A tattaunawar da mu ka yi, mun fahimci cewa wannan ba abinda za a ɓata lokaci mai tsawo bane a kansa, shiyasa za mu sake zama a ranar Talata, domin cire tallafin yana da illa musamman ga marasa ƙarfi sosai."

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Gwamnan PDP Zai Yi Binciken Kwakwaf Kan Gwamnatin Da Ya Gada, Ya Bayyana Dalilansa

"Amma muna da hanyar magance hakan, saboda za a riƙa ajiye kuɗi waɗanda za a yi amfani da su ko kuma a ciyo bashi. Hakan sai zanya a inganta albashi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin. Ina ganin hakan bai saɓa doka ba."

Talaka Zai Samu Sauƙi, ‘Yan Kasuwa Sun Ce Farashin Man Fetur Zai Sauko Ƙasa

Rahoto ya zo cewa ƙungiyar ƴan kasuwar man fetur ta IPMAN ta yaba da matakin gwamnatin tarayya na amincewa a riƙa shigo da man fetur daga waje.

Ƙungiyar tace hakan zai sanya farashin man ya yo ƙasa warwas saboda rububin da ƴan kasuwa za su yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel