Kasar Sweden Ta Halasta Jima’i a Matsayin Daya Daga Wasannin da Ake Yi a Kasar

Kasar Sweden Ta Halasta Jima’i a Matsayin Daya Daga Wasannin da Ake Yi a Kasar

  • Kasar Sweden a duniyar turai ta bayyana amincewa da gasar saduwa da za a yi nan ba da jimawa ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa, za a dauki makwanni uku ana gudanar da gasar daga ranar 8 ga watan Yuni
  • Ba wannan ne karon farko da ake halast abubuwan da suka saba da addini da al’adar dan adam ba a duniyar turai

Sweden - Kasar Sweden ta ayyana jima’i a matsayin daga wasannin da ta halasta, kuma ta shirya tsaf don gudanar da gasar jima’i a mako mai zuwa, inji rahoton India Times.

A cewar rahotannin da muke samu daga kasashen waje, mutanen da za su gwabza a gasar za su yi jima’i ne na tsawon lokacin da ya kai sa’o’i shida a kowacce rana.

Wani kwamitin alkalan wasa ne zai bayyana wadanda suka yi nasara duba da ka’idojin da aka gindaya.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Yadda aka kirkiri gasar jima'i a turai
An kirkiri gasar jima'i a kasar Sweden | Hoto: npr.org
Asali: UGC

Adadin da zangon wasa daya a gasar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, an ce tsarin, wanda kungiyar hada gasar jima’i ta turai ta shirya yi a ranar 8 ga watan Yuni za ta dauki tsawon makwanni shida, kuma gasar wasa daya zai dauki mintuna 45 zuwa sa’a daya ne.

Haka nan, rahoton ya ce ‘yan kalli za su ba da gudunmawa wajen zaban wadanda suka yi nasara a wannan gasa irinta ta farko.

Abubuwan da za su duba wajen alanta mai nasara a wasan sun hada da shakuwa, kwarewa, ilimin jima’in da kuma juriya.

‘Kamasutra’

Ilimin ‘Kamasutra’, wanda ya shahara a addinin Hindu da littatafansu zai yi tasiri matuka wajen yanke shawarin masu nasara a gasar, rahoton Live Mint.

Kamasutra dai tsagwaron sani ne a fannin ilimi saduwa a addinin Hindu, wanda kuma zai zama ma’auni a gasar ta kasar Sweden.

Kara karanta wannan

Assha: Ta yi aure da nufin jin dadi, ta shiga rudani saboda halin mijinta dan wata jiha

Bugu da kari, gasar ta ba da dama ga kowane tantiri a fannin saduwa zai iya halarta don baje-kolin tsagwaron kwarewa a saduwa.

Wai hakan ci gaba ne

Da suke bayyana jin dadinsu da samun ci gaba – mai kama da na mai tonon rijiya – wadanda suka shirya gasar sun ce wannan babbar nasara ce ga duniyar wasanni, musamman a turai.

Wani rahoton da muka samo ya bayyana shawari ga adadin lokutan da ya kamata ma'aurata suke jima'i.

Asali: Legit.ng

Online view pixel