Sabuwar Gwamnati: Jerin Sunayen Wadanda Tinubu Ya Ba Wa Mukami a Makonsa Na Farko

Sabuwar Gwamnati: Jerin Sunayen Wadanda Tinubu Ya Ba Wa Mukami a Makonsa Na Farko

  • An rantsar da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu a filin taro na Eagle Square da ke Abuja
  • Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya yi nasara a babban zaben da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara
  • Tun bayan hawan nashi karagar mulki, Bola Tinubu ya nada wasu muhimman mukamai a makonsa na farko a kan kujera

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya karbi rantsuwa a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja.

Tun bayan karbar rantsuwar, tsohon gwamnan jihar Lagos, Tinubu ya nada wasu mukamai a matsayinsa na shugaban kasa.

Jerin Sunayen Masu Mukamai
Jerin Sunayen Wadanda Tinubu Ya Bai Wa Mukani a Makonsa Na Farko. Hoto: @BayoOmoboriowo, @dipoaina1, @DOlusegun, @SenatorAkume.
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro jerin sunayen wadanda Shugaba Tinubu ya bai wa mukamai daba-daban a makonsa na farko a matsayin shugaban kasa.

1. Kunle Adeleke: a matsayin babban mai tsare-tsare

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Shugaba Tinubu ya nada Victor Adekunle Adeleke a matsayin babban mai masa tsare-tsare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeleke yana da kwarewa sosai ta fannin diflomasiyya, indaya yi ayyuka da dama da suka kaishi kasashe da dama da Nahiyoyi.

Adeleke ya yi aiki a ma’aikatu da dama ciki har da ofisoshin jakadanci, Adeleke ya maye gurbin Hussaini Adamu wanda shi ne tsohon mai tsare-tsare na tsohon shugaba Buhari.

2. Olusegun Dada: a matsayin mai ba da shawara akan yada labarai na zamani

Shugaba Tinubu ya sake nada Olusegun Dada a matsayin mai bashi shawara na musamman akan yada labarai na zamani.

Dada ya maye gurbin Bashir Ahmad wanda shi ne ya rike mukamin a lokacin tsohon sugaban kasa Buhari.

Kafin nada shi mukamin, Dada shi ne shugaban bangaren sadarwa ta zamani na jam’iyyar APC.

Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikata na Gwamnatin Tarayya

Kara karanta wannan

Jita-Jita: Shin Tinubu Ya Nada Pat Utomi, Aminin Peter Obi Minista? Jigon Jam'iyyar Labour Ya Mai da Martani

Shugaba har ila yau, a ranar Juma’a 2 ga watan Yuni, Tinubu ya nada kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikata na Gwamnatin Tarayya.

Tabbatar da nada Femi ya kawo karshen cece-kuce da ake ta yi akan nadin nasa a kafofin yada labarai.

Sanata Ibrahim Hadejia: a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata

Sanata Ibrahim Hadejia, wanda shi ne tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, an nada shi a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata na Tinubu.

Sanata Hadejia yanzu haka sanata ne da yake wakiltar Arewa maso Gabas a jihar Jigawa.

George Akume: a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya

Shugaba Tinubu ya nada tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Akume, mai shekaru 69 ya kasance tsohon gwamnan jihar Benue da ke Arewa maso Tsakiyar Najreriya.

Nosa Semota: a matsayin mai daukar hoto na Tinubu

Matashi Nosa Semota ya ci gaba da rike mukamin mai daukar hoto na Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu ya dade da zaban Semota a matsayin mai daukar hotonsa tun farkon fara neman shugabancin kasar.

Rahotanni sun tabbatar cewa dan Shugaba Tinubu, Seyi Tinubu shi ne ya kai Semota don bashi wannan mukami.

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC, ta yi ganawar gaggawa da gwamnatin Tinubu game da cire tallafin mai.

Hausa.legit.ng ta lissafo abubuwa 5 masu muhimmanci da suke da alaka da ganawar da aka yi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel