Kwastoma Ya Sace Wa 'Yar Gidan Magajiya N92,300 Bayan Sun Gama 'Harka' A Abuja

Kwastoma Ya Sace Wa 'Yar Gidan Magajiya N92,300 Bayan Sun Gama 'Harka' A Abuja

  • Kotu da ke zamanta a birni tarayya ta gurfanar da wani mutum mai suna King Dauda bisa zargin satar makudan kudade
  • Ana zargin Dauda ne da satar makudan kudade har N92,300 na budurwarsa bayan sun kwana a gidansa da ke Life Camp
  • Mai gabatar da kara, Stanley Nwafoaku ya fada wa kotu ce wa Bolaji Olufumi ta kawo karar Dauda bisa zargin sata

FCT, Abuja – Jami'an ‘yan sanda a sun gurfanar da wani dan kasuwa mai suna King Dauda a gaban kotun yankin Kado da ke birnin tarayya Abuja.

Ana zargin King Dauda ne da ke unguwar Life Camp a birnin Abuja da satar makudan kudade har N92,300 na budurwarsa.

Kotun Najeriya
Kotu Ta Tasa Keyar Kwastoma Bayan Sace Kudi Har N92,300 Na Karuwarsa. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta tattaro cewa wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa akai.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ’Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ta Damfari Mutane Fiye da 100 Kudi Har N150m

Mai gabatar da kara, Stanley Nwafoaku ya fada wa kotu cewa a ranar 26 ga watan Mayu da misalin karfe 9:05 na safe, Bolaji Olufumi ta kawo kara a ofishin ‘yan sanda na Life Camp.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda abin ya faru, kamar yadda mai gabatar da kara ya fada

Mista Nwafoaku ya ce a ranar 20 ga watan, wanda ake zargin ya gayyaci wadda take karar gidansa, bayan sun kwana tare sai ya sace mata jakar kudinta karama da ke dauke da kudi N92,300.

Ya ce duk kokarin da ta yi don gano inda jakar take da kuma kudaden nata daga Dauda abin yaci tura.

Ya kara da cewa aikata hakan laifine a dokar kasa da ya sabawa sashe na 288 na kundin tsarin mulki a kasa.

Lauyan wanda ake karar ya nemi alfarmar beli

Lauyan wanda ake zargi, Charity Nwosu ya nemi alfarmar beli inda ya yi amfani da sashe na 36 na kundin tsarin mulki da kuma sashe na 158 na dokar aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Shin Sabon Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, Ya Ayyana Triliyan N9 a Kadarorinsa? Gaskiya Ta Bayyana

Nwosu ya tabbatar wa da kotu cewa wanda ake zargin ba zai saba ka’idojin beli ba idan aka ba shi.

Mai shari’a, Muhammad Wakili ya tabbatar da ba da belin akan kudi N100,000 da kuma wanda zai dauki belin nasa.

Wakili ya ce mai daukan belin dole zai kawo shaidar lambar banki ta BVN da kananan hotuna guda biyu da katin shaida aiki wanda sai kotun ta tabbatar da ingancinsa.

Mai shari’a, Muhammad Wakili ya dage sauraran karar har zuwa 15 ga watan Yuni don ci gaba da sauraran karar, cewar rahotanni.

Kotu Ta Datse Igiyar Auren Fasto Saboda Jibgar Matarsa, Ta Mallaka Wa Matar Kadarorinsa

A wani labarin, kotu ta datse auren wani Fasto bisa zargin cin zarafin matarsa da barazanar kisa.

Kotun na zargin Oni Muyiwa da yi wa matarsa barazanar zai kashe ta a lokuta da dama idan sun samu sabani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel