Kotu Ta Datse Igiyar Auren Malamin Addini Saboda Yawan Jibgar Matarsa, An Mallaka Wa Matar Dukkan Kadarorinsa

Kotu Ta Datse Igiyar Auren Malamin Addini Saboda Yawan Jibgar Matarsa, An Mallaka Wa Matar Dukkan Kadarorinsa

  • Wata kotu ta raba aure tsakanin ma’aurata saboda cin zarafi da barazana ga rayuwa da mijin ke yi wa matar
  • Wanda ake zargin mai suna Fasto Oni Muyiwa wanda ma’aikacin jinya ya saba cin zarafin mata daban-daban
  • Alkalin kotun ya umarci mijin ya mallakar wa matar gidansa da kuma filaye guda biyu da kuma motarsa

Jihar Ekiti - Wata kotun al’ada da ke zamanta a Ado-Ekiti da ke jihar Edo ta raba aure tsakanin mata da miji saboda cin zarafin matar da mijin ke yi da barazana ga rayuwarta.

Wanda ake zargin, Fasto Oni Muyiwa ya kasance ma’aikacin jinya wanda ke sakin mata yadda ya ga dama kuma mai auren jari.

Kotu a Najeriya
Kotu Ta Raba Auren Fasto Kan Cin Zarafi. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun Mista J.O Oyedele ya umarci ma’auratan da kowa ya kama gabansa ba tare da shiga harkan wani ba, cewar jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

Hukuncin alkalin kotun

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“An hana wanda ake zargin zuwa gidan mai karar bayan ya kwashe kayansa daga gidan.
“Rikon dan su guda kuwa, matar ce za ta daukeshi sai dai mijin yana iya zuwa wurin dan.
“Kotun ta kuma umarci wanda ake karan da ya damka wa matar motarsa kirar Toyota Camry ya zama mallakinta."

Hukuncin ya kara da cewa:

“Korun ta kuma umarci mijin da ya mallakar mata da gidansa da ke bayan makarantar nakasassu.
“Har ila yau kotun ta mallakar wa matar filaye guda biyu da ke yankin Idolofin, sannan takardar shidar mallakar filayen a saka sunan matar."

Yadda rikicin ya fara tsakaninsu

Wadda ta ke karar mai suna Madam Alabi Adejoke ta bakin lauyanta, Iyanu Olumuagun a ranar 11 ga watan Oktoba ta nemi a raba auren saboda mijinta ya umarceta ta bar gidanta sannan ya dawo mata da dukkan kayanta.

Kara karanta wannan

“Allah Ya Amsa Addu’arta”: Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Yi Wuff Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

A yayin bincike, an gano cewa mijin ba abin yarda ba ne kuma duk maganarsa karya ne.

Duk da haka, wadda take karar ta ce wanda ake zargin ba shi da mota amma ya samu motar ne ta dalilinta.

Sannan ta karyata mijin cewa shi kadai yake kula da ilimin yaron da kula sauran al’amuranshi.

Da Zarar Mijina Ya Ga ‘Skirt’, Sai Tsuminsa Ya Tashi, Matar Aure Ta Fadawa Alkali

A wani labarin, wata mata ta bukaci alkalin kotu da ya raba aurensu da mjinta saboda son mata.

Matar mai suna Oluwatoyin ta ce mijinta da zarar ya ga mata toh shikenan hankalinsa zai tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel