“So Suke Su Bata Mani Suna”: Gwamnan Zamfara Ya Magantu Kan Zargin Mallakar Kadarorin Triliyan N9

“So Suke Su Bata Mani Suna”: Gwamnan Zamfara Ya Magantu Kan Zargin Mallakar Kadarorin Triliyan N9

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal-Dare, ya yi watsi da rahotannin cewa ya ayyana naira triliyan 9 a kadarorinsa
  • Gwamna Lawal ya ce mutanen Zamfara ba za su dunga fuskantar matsalolin da suke fuskanta ba idan da yana da irin wannan makudan kudaden
  • Gwamnan Zamfaran ya bayyana cewa da ya yi amfani da kudin wajen ci gaban jihar idan da yana da shi

Gusau, Jihar Zamfara - Sabon gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi watsi da rahotannin cewa ya ayyana naira tiriliyan 9 na tsaba, kadarori da hannun jari da yake da su.

Da yake magana a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni a wata hira da sashin Hausa na Radiyo Faransa (RFI), Lawal ya ce makirai ne suka kirkiri rade-radin da ke yawo, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwastoma Ya Sace Wa 'Yar Gidan Magajiya N92,300 Bayan Sun Gama 'Harka' A Abuja

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal
“So Suke Su Bata Mani Suna”: Gwamnan Zamfara Ya Magantu Kan Zargin Mallakar Kadarorin Triliyan N9 Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Ya ce:

"Da ina da irin wannan kudin, duk matsalolin da mutanena ke fama da shi, zan yi amfani da kudin wajen magance matsalolin."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kadarorin Triliyan N9: Dauda Lawal ya dauki zafi kan makirai

Gwamnan ya koka kan lalacin wasu mutane wajen tabbatar da gaskiyar labari kafin su yarda da shi. Ya koka cewa wasu mutane na kokarin bata masa suna.

Lawal ya ce:

"Yanzu, wannan lamarin jawabi ne na jama'a kuma akwai kafa ga duk wanda ke son tabbatarwa ya zo ya yi hakan.
"Wannan ba komai bane face zargi da wasu makirau, wadanda ke son bata mani suna suka shirya."

Bugu da kari, Lawal ya roki Allah ya ba shi wannan makudan kudade "don na yi amfani da shi wajen taimakawa mutanena."

Mune sa'annin yinka ba mahaifinmu ba, Bashir El-Rufai ya caccaki Sanata Shehu Sani

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Bankin CBN Ya Karyata Labarin Karya Darajar Naira Zuwa N630/$1

A wani labari na daban, Bashir, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi wa tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, wankin babban bargo kan shaguben da ya yi wa mahaifinsa game da bayyana kadarorinsa na 2015 da 2023.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Sanata Sani ya zargi El-Rufai da barwa jihar Kaduna tarin bashi, duk da ikirarin da ya yi cewa bai taba wawure kudaden jihar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel