Shugaban NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Shugaban NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

  • Babban jami'in gudanarwar na Kamfanin NNPC na kasa Mele Kyari, ya bayyana cewa farashin da ake gani na man fetur a yanzu, yanayi ne na kasuwa ya zo da shi
  • Ya ce cire tallafin man fetur zai sanya a samu gasa tsakanin kamfanonin da ke hada-hadar mai a ƙasar nan
  • Kyari ya kuma ƙara da cewa farashin da ake gani a yanzu, ba dawwamamme ba ne, kasuwar za ta daidaita kanta

Babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) Mele Kyari, ya ce sabon farashin man fetur na yanzu zai iya sauka a kowane lokaci.

Kyari ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, a inda jaridar The Cable ta tsakuro bayanai daga ciki.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: NNPC Ya Fadi Sabon Shirin Bola Tinubu Tun da Farashi Ya Kai N550

Mele Kyari ya yi magana kan hauhawar farashin mai
Mele Kyari ya ce farashin man fetur zai daidaita kansa. Hoto: The Cable
Asali: UGC

Tinubu ya sanar da cire tallafi

A jawabinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayu, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa babu maganar ci-gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da dai masu taimakawa shugaban a kafafen watsa labarai, sun zo daga baya sun fayyace cewa, sai a wannan watan ne batun zai fara tasiri. Sai dai kafin ayi aune, farashin mai ya riga da ya yi tashin gwauron zabi.

Kamfanin NNPC, wanda ya goyi bayan sanarwar ta shugaba Tinubu, ya sanar da ƙara farashin man a kasuwannin kamfanin na ƙasa baki ɗaya.

Kamfanin man ya ce farashin da ake gani a yanzu, yanayin kasuwar ne ya zo da shi.

Kyari, a yayin tattaunawar, ya ƙara da cewa cire tallafin man fetur ɗin zai sanya gasa tsakanin kamfanoni, da kuma sassaita yadda ake amfani da shi, sannan ya ce sabon farashin man zai daidaita kansa.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur

A wani rahoto na Nigerian Tribune, Mele Kyari ya bayyana cewa akwai yiwuwar faɗuwar farashin man cikin sati biyu zuwa uku.

Kasuwar za ta daidaita kanta

A kalaman Kyari:

“Farashin da muke gani a yanzu, farashi ne na kasuwa. Abinda hakan ke nufi shi ne, farashin kasuwa na iya sauka a kowane lokaci kuma ba shakka kasuwar za ta daidaita kanta.”

Kyari ya kuma ce dole za a samu ƙaruwar kamfanoni da za su shiga hada-hadar ta mai, saboda wasu da ke ciki yanzu sun ƙi zura jiki sosai a harkar, saboda tunanin cewa sabuwar gwamnati ba za ta biya tallafi ba.

Sai dai ya ce a wannan farashin da kasuwa ta zo da shi yanzu, zai bai wa yan kasuwar damar shigo da man ko kuma su siya a cikin gida, sannan su siyar da shi a kasuwa yadda farashi ya kama.

Ba mu shirya ko wace iriyar zanga-zanga ba tukun

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Bankin CBN Ya Karyata Labarin Karya Darajar Naira Zuwa N630/$1

A wani labarin mai alaƙa da wannan, ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa (NLC) ta ce ba ta shirya gudanar da wata zanga-zanga ba a halin da ake ciki yanzu.

Sai dai ƙungiyar ta bayyana fushinta dangane da ƙarin farashin man da aka yi da ƙungiyar ta kira da ƙarin farashi na rashin lissafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel