Uba Sani Ya Yi Ganawar Farko Da Jami'an Tsaro a Kaduna, Sun Tattauna Kan Matsalar Rashin Tsaron Jihar

Uba Sani Ya Yi Ganawar Farko Da Jami'an Tsaro a Kaduna, Sun Tattauna Kan Matsalar Rashin Tsaron Jihar

  • Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi alƙawarin samar da kayan aikin da suka dace ga hukumomin tsaron jihar domin gudanar da ayyuka yadda ya kamata
  • Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin ta samar da tsaro ga al'ummar jihar da a yanzu suke fama da matsananciyar barazanar tsaro
  • Gwamnan ya yi kira da a ƙaddamar da tsarin tsaro na bai ɗaya ta hanyar inganta cuɗanya da jama'a gami da wayar da kan al'umma kan muhimman bayanan tsaro

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gana da shugabannin hukumomin tsaro don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsaro a jihar ta Kaduna.

Gwamnan ya sha alwashin samar da dukkan kayan aikin da suka dace ga hukumomin tsaro domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a jihar, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

Uba sani ya gana da jami'an tsaro a Kaduna
Uba Sani ya sha alwashin bai wa jami'an tsaro duk kayayyakin da suke bukata. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Uba Sani zai maida hankali sosai kan matsalar tsaro

Gwamnan, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren watsa labaran sa, Muhammad Lawal Shehu, ya bayyana damuwarsa tare da jaddada cewa tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya buƙaci shugabannin hukumomin tsaro da su samar da wani shiri na tsaro na bai ɗaya domin shigo da al'umma cikin hidimar saboda wayar musu da kai kan batutuwan da suka shafi tsaro.

A nasu bangaren, shuwagabannin hukumomin tsaro sun bai wa gwamnan tabbacin cewa za su jajirce wajen ganin an samu zaman lafiya a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro, musamman kananan hukumomi takwas da matsalar ta fi ƙamari da sauran su.

An tattauna manyan batutuwan tsaron jihar a taron

Kara karanta wannan

Yadda Ma’aikatu Suka Yi Bindiga da Naira Tiriliyan 3.8 a Karkashin Mulkin Buhari

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa an tattauna batutuwan ƙalubalen tsaro da suka haɗa da batun ayyukan ‘yan fashin daji, garkuwa da mutane, rikicin ƙabilanci, ƙwacen waya, barazanar karancin man fetur, fadan ‘yan daba (sara suka) da kuma ƙarancin wutar lantarki da jami’ar Ahmadu Bello Zaria ke fuskanta.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da shugabannin hukumomin tsaron sojojin Najeriya, rundunar ‘yan sandan Najeriya, rundunar sojan sama, ma’aikatar tsaro ta ƙasa, makarantar fasahar makamai ta sojojin ruwa, jami’an tsaro na NSCDC da kuma yan bijilantin jihar Kaduna.

INEC ta tabbatarwa da Uba Sani nasarar lashe zaɓe

A labarinmu na baya, kun ji cewa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta shaidawa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe cewa sabon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ne ya lashe zaɓen da ya gudana a watan Maris.

Hakan dai na zuwa ne biyo bayan wani kuskure da hukumar zaɓen ta ce ta gano cikin ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Isa Ashiru Kudan suka shigar na ƙalubalantar nasarar ta Uba Sani.

Kara karanta wannan

Daga Fara Mulki, Korafi Ya Fara Fitowa, Abba Gida-Gida Ya Koka Kan Karancin Ruwa a Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel