Bikin Rantsar da Abba Gida Gida: Rundunar ’Yan Sanda Ta Kama Masu Laifi 93 a Cikin Mako Guda

Bikin Rantsar da Abba Gida Gida: Rundunar ’Yan Sanda Ta Kama Masu Laifi 93 a Cikin Mako Guda

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama akalla mutane fiye da 90 a kasa da mako guda da ake zarginsu da aikata laifukan ta'addanci
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammed Usaini Gumel ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jaridu
  • Ya ce a binciken da suka gudanar akan wadanda ake zargin, ya tabbata cewa sun yi shirin kawo cikas a bikin rantsar da sabon gwamna

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutane 93 da ake zargi da laifuka daban-daban a cikin kasa da mako guda a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammed Usaini Gumel ne ya tabbatar da haka yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Laraba 31 ga watan Mayu.

Wadanda ake zargi
Rundunar ’Yan Sanda Ta Kama Akalla Masu Laifi 93 a Kano. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Gumel ya ce binciken farko ya tabbatar da zargin da ake yi akan wadanda aka kaman, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

‘Mutane Sun Iya Karya’: Gwamnatin Anambra Ta Ce Ba a Wulakanta Gwamnanta a Rantsar da Tinubu Ba, Ganduje Fa?

Ana zarginsu da shirya tada zaune tsaye a bikin rantsarwa

Ya ce daga cikin zarge-zargen da ake musu akwai kawo cikas da kuma daukar nauyinsu da aka yi don su kawo tarnaki yayin bikin kaddamar da sabuwar gwamnati ta Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa, an samu wasu daga cikin wadanda ake zargin da muggan makamai a tare da su don aiwatar da laifukansu, cewar Vanguard.

Matasan suna cikin maye lokacin da aka kama su

Ya ce abin bakin ciki da tashin hankali shi ne yadda suke a cikin maye don aiwatar da duk abin da suka yi niyya akan al’umma da suka hada da fashi da kwace da kuma kawo cikas a wurin taron.

A cewarsa:

“Duk wadanda muke zargin, za a gurfanar da su a gaban kotu akan abin da ake tuhumarsu.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

“Ina da kwarin gwiwar cewa kotu za ta dauki matakin da ya dace akansu don zama izina ga masu shirin aikata irin wadannan laifuka.”

Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Matashi Da Ya Halaka Mahaifiyarsa a Kano

A wani labarin, Rundunar 'yan sandan jihar Kano sun yi nasarar cafke wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa a Kano.

Matashin, mai suna Ibrahim Musa ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 50 a Rimin Kebe da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel