Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

  • A daidai lokacin da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ke gama jawabi, matakalar bikin rantsar da shi ta ruguje kasa a taron
  • Rahotanni sun bayyana yadda jami’an tsaro ciki har kwamishinan ‘yan sanda suka tallafi gwamnan don komawa wurin zaman manyan baki
  • Har ila yau, Sarkin Kano, Aminu Bayero da na Bichi Nasiru Bayero basu samu tarba mai kyau ba yayin da jama’a suka musu ihu a wurin taron

Jihar Kano – A yayin rantsar da sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf matakalar taron ta rushe jim kadan bayan an rantsar da gwamnan.

A daidai lokacin da sabon gwamnan ke barin kan matakalar ne ta ruguje, daidai sadda yake komawa wurin da manyan baki ke zaune.

Abba Kabir
Sabon Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Premium Times ta tattaro cewa jami’an tsaro sun tallafi gwamnan tare da kwamishinan ‘yan sanda, Ahmed Gumel a lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Babu Sa'a: Mutane Sun Fadi Ra'ayinsu Yayin Da Ruwan Sama Ya Cika Inda Tinubu Zai Karbi Rantsuwa

Har ila yau, gwamnan bai samu damar duba faretin jami’an tsaro ba saboda yadda jama’a suka yi tururuwa a cikin filin wasan na Sani Abacha da ke birnin Kano.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane sun yi tururuwa a filin rantsarwa, an yiwa sarakuna ature

An gagara hana dandazon jama’a shiga cikin filin wasan wadanda suka kasance magoya bayan jam’iyyar NNPP ne ko wannensu sanye da jar hula, yayin da suka yi wa Sarkin Kano da Bichi ihu.

Rahotannni sun tabbatar da cewa bayan ihun da aka yi wa Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma Nasiru Bayero, wasu har da jifansu suke da robar ruwa a wurin taron, cewar jaridar Daily Trust.

Taron wanda aka kammala shi da misalin karfe 11 na safe, har lokacin tattara wannan rahoto jami’an tsaro suna can suna ta neman hanyar da za su fitar da sarakunan cikin aminci.

Kara karanta wannan

Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis

'Yan Kwankwasiyya na zargin sarakunan suna tare da gwamnatin APC da ta sauka a mulki

‘Yan Kwankwasiyya kamar yadda ake kiran magoya bayan jam’iyyar NNPP, suna zargin cewa dukkan wadannan sarakuna suna tare da gwamnatin APC da ta sauka daga mulki.

An Yi Wa Sarkin Kano Ihu A Wurin Bikin Rantsar Da Abba Gida Gida

A wani labarin, An yi wa Sarkin Kano ihu a yayin taron ratsar da Abba Kabir Yusuf a wurin taro na Sani Abacha da ke Kano.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika mulki ga sabon gwamna, Injiniya Abba Kabir a yau Litinin 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel