'Yan Sanda Sun Cafke Matashi Da Ya Halaka Mahaifiyarsa a Kano

'Yan Sanda Sun Cafke Matashi Da Ya Halaka Mahaifiyarsa a Kano

  • Rundaunar ‘yan sanda ta yi nasarar cafke wani matashi da ake zargin ya daba wa mahaifiyarsa wuka a jihar Kano
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan a jihar, SP Abdullahi Haruna ne ya sanar da haka a ranar juma’a 5 ga watan Mayu
  • ‘Ya’yar wanda ake zargin ta ce Ibrahim daman ya na fama da matsalar kwakwalwa, kuma yafi shekara guda ba ya zuwa wurin da suke.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sanda ta kama wani yaro, Ibrahim Musa da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa mai kimanin shekaru 50 a Rimin Kebe cikin karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano.

Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna ne ya ba da wannan sanarwar a ranar juma’a 5 ga watan Mayu, Daily Trust ta tattaro.

Ibrahim Musa
Matashin Da Ya Kashe Mahaifiyarsa a Kano, Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wanda ake zargin an kama shi ne a wata mabuya ta masu aikata munanan laifuka a karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Basaraken Da Ya Yi Barazanar Kawo IPOB Legas

Rhotanni sun tabbatar cewa wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin, kuma za a tasa keyarsa zuwa kotu bayan an gama bincike.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take bayanin yadda al’amarin ya faru, ‘ya’ayar wanda ake zargin ta ce:

“Ya share fiye da shekara guda ba tare da ya zo in da muke ba, kawai sai muka ganshi misalin karfe 5:30 na yamma”.
“Ya na rayuwa ne da mahaifinsa a Kurna bayan ya sha fama da matsalar kwakwalwa, kwatsam sai gashi nan ya shigo gidan ya na tambayar mahaifiyarmu”.
“Da ya tambaya ko tana nan aka ce ta shiga makota sai ya sa aka kirata, ta shigo ta na fara’a da ta ganshi, sai muka ji ta kurma ihu ashe wuka ne a hanunsa”.
“Ni ma ya yi kokarin kaimin hari amma na gudu, a lokacin ne mutane suka kawo mana dauki, shi kuma sai ya jefar da wukan ya gudu”.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Matashin Saurayi Ya Burma Wa Mahaifiyarsa Wuƙa Har Ta Mutu a Kano

‘Ya’yar wanda ake zargin ta kara da cewa:

“Marigayiyar ta saba kai masa ziyara duk lokacin da ta yi mummunan mafarki da ya shafe shi, zuwan ta na karshe a watan azumi korar kare ya mata da kyar ta tsira bayan mutane sun kawo mata dauki”.

'Yan sanda a jihar Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane da dama

Rundunar ‘yan sanda a Kano sun yi nasarar bindige wasu masu satar mutane a kalla uku tare da ceto wasu mutane bayan an yi garkuwa da su a jihar.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna ne ya tabbatar da faruwar lamarin a Kano a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an kashe masu garkuwar ne a wani artabu da ya barke tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel