'Yan Bindiga Sun Sace Shugabannin Matan Jam'iyyar APC Bayan Sun Halarci Rantsar Da Uba Sani a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Shugabannin Matan Jam'iyyar APC Bayan Sun Halarci Rantsar Da Uba Sani a Kaduna

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan sun sace shugabannin matan jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Gwari bayan sun halarci rantsar da Uba Sani
  • Har ya zuwa yanzu dai ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalsn waɗanda suka sace ɗin ba domin sanin halin da suka samu kansu a ciki

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun sace wasu shugabannin mata na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna.

Shugabannin matan na jam'iyyar APC an yi awon gaba da su ne a wajen Manini na ƙaramar hukumar Birnin Gwari, bayan sun halarci bikin rantsar da sabon gwamnan jihar, sanata Uba Sani.

'Yan bindiga sun sace jiga-jigan jam'iyyar APC a Kaduna
Tsautsayi ya ritsa da jiga-jigan ne bayan sun dawo daga rantsar da Uba Sani Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Shugaban ƙungiyar Birnin Gwari Emirate Progressive Union (BEPU), Ishaq Usman Kasai, shine ya bayyana hakan ya yin tattaunawa da jaridar Tribune a ranar Laraba da safe.

A cewarsa ƴan bindigan sun tare hanyar ne, sannan suka sace shugabannin matan biyu na jam'iyyar APC, da kuma wasu mutane da dama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana shugabannin matan na jam'iyyar APC da aka sace su ne, shugabar matan jam'iyyar APC ta ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Hajiya Lami Awarware da mataimakiyarta, Hajiya Haulatu Aliyu.

Ƴan bindigan sun tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji

Rahotanni sun tabbatar da cewa, ƴan bindigan na sace su a ranar Talata, suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Ya kuma bayyana cewa, har ya zuwa yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalansu ba, ko wani daban a yankin.

A cikin ƴan kwanakin nan, ƙungiyar BEPU a saƙon taya murna ga sabon shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ta roƙe shi da ya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin.

Haka kuma har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, gwamnatin jihar da rundunar ƴan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba, dangane da lamarin.

Yan Bindiga Sun Dira Birnin Gwari a Jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun yi wa garin Birnin Gwari ƙawanya, inda suka sace mutane da dama.

Ƴan bindigan dai sun gudu daga jihar Zamfara bayan jami'an tsaro sun fatattako su daga can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel