Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'addan ISWAP a Jihar Borno

Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'addan ISWAP a Jihar Borno

  • Dakarun sojoji na rundunar ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasarar tura wasu ƴan ta'addan ISWAP zuwa inda ba a dawowa
  • Dakarun sojojin sun tura ƴan ta'addan zuwa barzahu a yayin wani sintiri da suka fita a wani yanki da ke iyaka da tafkin Chadi
  • Wani daga cikin sojojin ya samu rauni a yayin artabun da sojojin suka yi da ƴan ta'addan, inda aka garzaya da shi asibiti domin ba shi kulawa

Jihar Borno - Dakarun sashi na uku na rundunar sojin tsaro ta ƙasa da ƙasa (MNJTF), sun halaka ƴan ta'addan ƙungiyar Islamic State of the West Africa Province (ISWAP) mutum uku a jihar Borno.

Zagazola Makama, wani majiya wanda ya mayar da hankali kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun baƙunci lahira ne a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Sake Kai Mummunan Hari Kan 'Yan Sanda a Jihar Ebonyi, Sun Halaka Da Dama

Dakarun sojoji sun halaka 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Dakarun sojoji Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Dakarun sojojin sun haɗu da ƴan ta'addan ne lokacin da su ke sintiri a tsakanin iyakar tafkin Chadi da Malam Fatori, cikin ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Wata majiyar sirri ta bayyana cewa ƴan ta'addan sun gamu da ajalinsu ne a hannun dakarun bataliya ta 86 ta rundunar MNJTF.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakarun sojojin sun ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan

Majiyar ta bayyana cewa, dakarun sojojin sun kwato bindigu guda biyu ƙirar AK-47 a hannun ƴan ta'addan, inda ta ƙara da cewa wani soja guda ɗaya ya samu rauni a yayin musayar wutar, cewar rahoton The Cable.

An kai jami'in sojan da ya samu rauni zuwa asibitin sojoji a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin duba lafiyarsa.

Yan Ta’addan ISWAP Sun Yiwa Dakarunsu da Sojojin Najeriya Suka Kashe Jana’iza

Kara karanta wannan

Tun Kafin Ya Shiga Ofis, Sarakunan Yarbawa Sun Gabatar Da Bukatunsu Ga Bola Tinubu

A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda dakarun sojoji suka halaka ƴan ta'addan ƙingiyar ISWAP da dama a jihar Borno, da ke a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ƴan ta'addaɓ na ƙungiyar ISWAP sun taru a waje ɗaya domin yi wa ƴan'uwan su waɗanda suka haɗu da ajalinsu a hannun dakarun sojoji, jana'iza. Adadin yawan ƴan ta'addan da suka baƙunci lahira ya kai 60.

Asali: Legit.ng

Online view pixel