'Yan Bindiga Sun Dira Birnin Gwari a Jihar Kaduna, Sun Sace Mutane Da Dama

'Yan Bindiga Sun Dira Birnin Gwari a Jihar Kaduna, Sun Sace Mutane Da Dama

  • Ƴan bindiga da suka tserro daga jihar Zamfara, sun dira Birnin Gwari cikin jihar Ƙaduna inda suka yi awon gaba ɗa dama
  • Ƴan bindigan sun shiga har cikin garin Birnin Gwari sannan suka sace mutanen da basu san hawa ba basu san sauka ba
  • Harin da ƴan bindigar suka kai ya sanya an ƙaƙaba dokar taƙaita lokacin zirga-zirgar mutane a yankin Birnin Gwari

Jihar Kaduna - Al'ummar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun bayyana cewa, ƴan bindiga da suka tsero daga jihar Zamfara sun kewaye garin, sannan suka yi awon gaba da mutane da dama.

Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da daddare, a yankin Gobirawa cikin Birnin Gwari, wanda ya ke a kusa da NTA Birnin Gwari. Wajen bai kai nisan mita 500 da wajen da sojojin sama suka yada zango ba, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Dab Da Rantsar Da Shi

'Yan bindiga sun sace mutane da dama a Birnin Gwari
'Yan bindigan sun tsero ne daga jihar Zamfara Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin-Gwari, Abdullahi Ibrahim Muhammad Amir, ya gargaɗi mutanen yankin da su taƙaita zirga-zirgar da su ke yi a cikin yankin Birnin Gwari.

Ya dai yi wannan gargaɗin ne bayan kammala taro tsakanin shugabannin masarautu da jami'an tsaro na yankin. Shugaban ya bayyana cewa an haramta tafiya akan ƙafa, babur ko mota daga ƙarfe 8:30 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta gaza wajen magance matsalar tsaro a yankin

Darektan hukumar watsa labarai ta jihar Kaduna, Alhaji Zubair Abdurra’uf, wanda ya tattauna da manema labarai da yammacin ranar Juma'a, ya bayyana cewa lokacin da ya ankarar da cewa ƴan bindiga na ƙara matsowa zuwa Birnin Gwari, mutane da dama ba su yarda da shi ba.

Abdurra’uf ya nuna ɓacin ransa kan yadda tsaurin idon ƴan bindigan ya kai har su shigo cikin garin Birnin Gwari, su aikata wannan ɗanyen aikin.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Kwabe: 'Yan Bindiga Sun Sace Wani Fitaccen Malamin Addini a Kudancin Najeriya

Ya cacccaki gwamnati kan yadda ta kasa kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Birnin-Gwari, inda ya buƙaci yakamata a yi taro kan matsalar tsaro a yankin.

Ya kuma yi nuni da cewa ƴan bindiga sun ƙwace gonakin mutane a yankin tsakiyar Birnin Gwari, wanda hakan ya sanya noma ba zai yiwu ba a yankin.

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Fasto a Jihar Imo

A wani rahoton na daban kuma, ƴan bindiga sun sace wani babban faston ɗariƙar Katolika a jihar Imo, da ke a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Rev Fr Michael Opara, ya faɗa hannun ƴan bindigan ne lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida, bayan ya yi wata tafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel