Ma’aikatar Gwamnati Ta Samu Sabon Shugaba Ana Saura Awa 96 Buhari Ya Sauka

Ma’aikatar Gwamnati Ta Samu Sabon Shugaba Ana Saura Awa 96 Buhari Ya Sauka

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a nada sabon shugaba a hukumar NACETEM a Osun
  • Sanarwar nadin ta fito daga teburin karamin Ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire na tarayya
  • Olushola Odusanya ya na da shaidar digirin PhD a kasar waje, kuma yana koyarwa a jami’o’i

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya amince da nadin Olushola Odusanya a matsayin Darekta Janar na hukumar NACETEM.

Kamar yadda labari ya zo daga Tribune, sanarwar nadin ta fito daga ofishin karamin Ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Mista Henry Ikoh.

Takardar nadin mukamin ta nuna wa’adin sabon Darekta Janar din ya fara daga ranar 13 ga watan Mayu, a wani kaulin an ce 1 ga watan Mayu.

Olushola Odusanya
Dr. Olushola Odusanya Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Kafin zamansa Darekta Janar, rahoton ya ce Olushola Odusanya Darekta ne a wani sashe na babbar cibiyar binciken kimiyya da fasaha na Sheda a Abuja.

Kara karanta wannan

Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika Odusanya ne Shugaban farko na gungun wasu masu bincike a cibiyar SHESTCO.

Olushola Odusanya ya na da PhD

Darekta Janar din rikakken ‘dan Boko ne, ya samu digirinsa na PhD a bangaren kimiyya da fasahar abinci a 1999 daga jami’ar Saints a kasar Malesiya.

A wani jawabi da hukumar ta fitar, ta ce sabon Darektan malamin ziyara da ke koyar da daliban da ke karatun zama Injiyoyi a jami’ar Princeton a Amurka.

Pulse ta ce sabon Darektan ya kai matakin mataimakin Farfesa a fanninsa a jami’ar kimiyya da fasaha ta Afrika wanda aka fi sani da AUST a birnin Abuja.

Masanin ya shafe shekaru fiye da 20 ya na bincike a kan bangaren fasahar jinsi, ya bada gudumuwa a fannin da takardu fiye da 50 da ya rubuta a Duniya.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Buhari 14 Da Aka Fi Damawa Da Su A Gwamnatin Tarayya Daga 2015 Zuwa Yanzu

An kafa hukumar NACETEM ne domin kula da harkar fasaha, cibiyar ta na Ile Ife a jihar Osun. Nan da ‘yan sa’o’i kadan za a canza gwamnati a Najeriya.

Nadin mukamin yana cikin na karshe-karshe da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi.

Shari'ar zaben 2023

Rahoto ya zo cewa Lauyoyin jam’iyyar PDP sun daukaka kara a kotun koli, su na so a soke takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben shugaban kasa.

A ranar Juma’ar nan za a yanke hukuncin karshe a kan takarar Kashim Shettima wanda ake zargin ya nemi mukamai biyu a jam'iyyar APC a zaben bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel