Rashin Tsaro, Tabarbarewa Tattalin Arziki Da Wasu Lamura 2 Da Suka Addabi Gwamnatin Buhari

Rashin Tsaro, Tabarbarewa Tattalin Arziki Da Wasu Lamura 2 Da Suka Addabi Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin Buhari-Osinbajo karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki zai zo karshe a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023
  • Gabannin mika mulki, abubwa da dama sun faru a gwamnati mai ci kuma yan Najeriya na duba zuwa ga gwamnati mai zuwa
  • Wannan labari na Legit.ng ya gabatar da wasu batutuwa da suka haifar da takaddama a gwamnatin Buhari

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo za su mika shugabanci ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar Litinin.

Shugaba Buhari da Osinbajo
Rashin Tsaro, Tabarbarewa Tattalin Arziki Da Wasu Lamura 2 Da Suka Addabi Gwamnatin Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Manyan batutuwan da suka haifar da takkadama a karkashin gwamnatin Buhari

Idan aka yi duba ga shekaru takwasa na gwamnati mai ci, abubuwa da dama sun faru a siyasar kuma wasu daga cikin wadannan batutuwa sun yi tasiri sosai a rayuwakan yan Najeriya yayin da wasu suka zama barazana ga rayuwarsu na yau da kullun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gabannin bikin rantsar da sabuwar gwamnati mai zuwa, Legit.ng ta tattara jerin wasu batutuwa da suka kawo karan tsaye ga gwamnatin Buhari, wanda yan Najeriya suka zata zai zamo mai ceto a garesu amma suka sha kunya.

1. Rashin tsaro

Tayar da kayar baya da kungiyoyin Boko Haram da na ISWAP suka dunga yi a yankin arewa maso gabas ya yi barazana ga kasancewar gwamnati mai shirin karewa.

Ya yi alkawarin murkushe kungiyar Boko Haram da na ISWAP tun bayan zabensa a watan Maris din 2015, amma sai sace-sacen mutane da rikicin makiyaya suka zama ruwan dare a karkashin gwamnatin Buhari.

2. Tabarbarewa tattalin arziki

Yaki da ta'addanci da faduwar farashin mai ya yi illa ga tattalin arzikin Najeriya.

Buhari ya yi alkawarin magance lamura da dama da suka shafi tattalin arzikin kasar kama daga zuba jari a harkar noma da abubuwan more rayuwa, amma farashin kayayyaki na tashi a kullun kwanan duniya.

Manufar babban bankin Najeriya musamman sauya fasalin naira bai taimakawa kasar da komai ba, maimakon haka ya jefa mutane cikin kangi, faduwar darajar Naira kuma ya kasance babban lamari har yanzu.

3. Yawan bashi

Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ciyo bashi fiye da abun da ta tara.

A zahirin gaskiya, wannan gwamnatin ta kara yawan kudaden da gwamnatin tarayya ta ranto daga waje wanda ya kara yawan basussukan da ake bin Najeriya.

Wannan babban lamari ya tayar da kura a kasar yayin da yan Najeriya suka bukaci a gudanar da bincike kan yadda ake kashe kudaden da aka ranto da kuma dalilin ranto su; hakan ya kasance ne yayin da ofishin kasafin kudin kasar ya ja hankali game da hauhawan bashin Najeriya. Ya kuma bayyana cewa idan har ba a yi wani abu ba zaici gaba da tabarbarar da tattalin arzikin kasar.

4. Cin hanci da rashawa

Yaki da cin hanci da rashawa shine babban alkawarin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daukarwa yan Najeriya a 2015.

Abun mamaki, sai ga shi cin hanci da rashawa ya yi katutu a gwamnati mai ci, koda dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na kan lamarin, amma dai an ce har yanzu ba a hukunta manyan jami'an gwamnati da suka fada komadarsu ba.

A cikin abubuwan da ke ta faruwa, yan Najeriya na sa ran ganin haske a gaba, musamman yayinda zababben shugaban kasa Bola Tinubu zai karbi ragamar kula da al'amuran kasar a ranar Litinin, 2q9 ga watan Mayu.

Buhari ya gaza dole a fada masa, Ortom

A wani labari na daban, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza kuma dole a fada masa.

Ortom ya ce ba a taba yin lalatacciyar gwamnati kamar wannan ba a tarihin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel