Nade-naden Mukamai Da Wasu Abubuwa 3 Da Tinubu Zai Fara Yi Bayan Rantsar Da Shi

Nade-naden Mukamai Da Wasu Abubuwa 3 Da Tinubu Zai Fara Yi Bayan Rantsar Da Shi

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya shirya karbar mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda wa'adinsa zai kare a ranar 29 ga watan Mayu.

Gabannin nasararsa a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, Tinubu ya sha gwagwarmaya iri-iri, a ciki da wajen jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya mai jiran gado
Nade-naden Mukamai Da Wasu Abubuwa 3 Da Tinubu Zai Fara Yi Bayan Rantsar Da Shi Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A lokaci guda, Tinubu ya kulla kawance da dama wadanda suka taimaka wajen nasarar da ya samu kuma suna iya kawo sauyi ga gwamnatinsa wacce za ta fara a ranar Litinin.

Sai dai kuma, akwai wasu muhimman matakai 5 da Tinubu zai dauka da zaran ya hau kujerar shugabancin kasa a ranar Litinin.

An jero wadannan muhimman abubuwa a kasa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Komawa fadar shugaban kasa

Kara karanta wannan

Malami, Emefiele Da Wasu Yan Majalisar Buhari Da Za a Ji Su Shiru Da Zaran Tinubu Ya Karbi Mulki

Abu na farko da ake sanya ran Tinubu zai yi a ranar Litinin bayan rantsar da shi a Eagles Square shine komawa fadar shugaban kasa kai tsaye.

A matsayin zababben shugaban kasa, an mayar da shi 'Defence House' a Abuja, inda yake samun wasu kulawa na shugaban kasa gabannin rantsar da shi.

Jawabai

Da isarsa fadar shugaban kasa, ana sanya ran sabon shugaban kasar zai samu jawabai daga dukkanin ma'aikatu da sassa a wannan rana ta Litinin.

Koda dai an tattaro cewa ya samu wasu jawabai a gidan tsaro amma ba kamar yadda zai samu ba a ranar Litinin.

Nada mambobin majalisarsa

A matsayin sabon shugaban kasa, ana sanya ran Tinubu zai sanar da nade-naden wasu yan majalisarsa, ba lallai ministoci ba.

Misalin yan majalisar da ake sanya ran Tinubu zai sanar a ranar Litinin sun hada da hadiman labaransa, shugaban ma'aikatansa da sauransu.

Haduwa da ma'aikatan fadar shugaban kasa

Kara karanta wannan

May 29: Jerin Yan Gwamnatin Buhari Da Tinubu Ka Iya Ci Gaba Da Tafiya Da Su Da Dalili

Tinubu dan siyasa ne da ke son gina alaka ba wai da manyan mutane ba harma da yan kasa.

Duba ga yanayinsa, ana sanya ran Tinubu zai hadu da kananan ma'aikata na fadar shugaban kasa duk da tarin kalubalen da ke gabansa.

Malami da wasu yan majalisar Buhari da Tinubu ba zai iya aiki da su ba

A baya mun kawo cewa gabannin karewar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, akwai wasu yan majalisarsa da ake ganin ba za su samu shiga gwamnati ta gaba ba.

Za a dai rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel