“Ya Gaza Sosai”: Bayan Ya Yafewa Buhari, Ortom Ya Yi Wa Shugaban Kasa Mai Barin Gado Wankin Babban Bargo

“Ya Gaza Sosai”: Bayan Ya Yafewa Buhari, Ortom Ya Yi Wa Shugaban Kasa Mai Barin Gado Wankin Babban Bargo

  • Har yanzu Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue na cike da dacin rai a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • A kwanaki gwamnan wanda ya kasance dan PDP ya bayyana cewa ya yafewa shugaban kasar mai barin gado
  • A yayin kaddamar da wani aiki a Makurdi, babban birnin jihar Benue, Ortom ya bayyana Buhari a matsayin shugaban kasa mafi muni a tarihin Najeriya

Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wacce ta gaza, yana mai cewa "ya zama tole a fada masa cewa ya gaza sosai kuma yan Najeriya na jin radadin gazawarsa saboda duk muna wahala."

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Ortom ya bayyana hakan ne yayin da yake kddamar da yan sa kai na jihar Benue (BSCVGs) a Makurdi.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Gabatar da Muhimmiyar Buƙata Ga Gwamnatin Tarayya Ana Gab da Rantsar da Tinubu

Shugaba Buhari da Samuel Ortom
“Ya Gaza Sosai”: Bayan Ya Yafewa Buhari, Ortom Ya Yi Wa Shugaban Kasa Mai Barin Gado Wankin Babban Bargo Hoto: @MBuhari, @GovSamuelOrtom
Asali: Twitter

Ya ce:

"Cin hanci da rashawa ya yi kamari a wannan gwamnati, duk da haka ana jefa mutanen da suka saci kaza kurkuku, amma mutanen da ke gwamnati sun mayar da hankali wajen satar kudaden jama'a suna yawo hankali kwance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A kwanaki shugaban kasar ya ba yan Najeriya hakuri, mun hakura amma ya zama dole a fada masa cewa ya gaza ba kadan ba kuma yan Najeriya na jin tasirin gazawar saboda duk muna wahala."

Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa Ortom ya yi zargin cewa barayi na zaune ne a gidan gwamnati.

Gwamna Ortom ya kuma bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta jefa yan kasa a kangin talauci da wahala idan aka kwatanta da yadda abun yake a gwamnatin magabacinsa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ortom wanda ya tuna aikin da ya yi karkashin tsohon shugaban kasar ya ce:

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

"Na yi aiki a karkashin gwamnatin shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma duk mun ga yadda Najeriya ta inganta karkashin wannan gwamnati. Duk mun san yadda farashin kayayyaki yake a wancan lokacin.
"Mun kuma san nawa farashin chanji yake a wancan lokacin da yadda yake a yau..Magana ta gaskiya ita ce a tarihin Najeriya ba mu taba fuskantar lalatacciyar gwamnati irin wannan ba a kasar."

Gwamnan ya kuma caccaki shugaba Buhari saboda gazawarsa wajen daidaita rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Gwamna Ortom ya ce ba zai taba kasancewa mai bangarenci ba domin zai ci gaba da caccakar rashin adalci a kasar.

Na shirya amsa gayyatar EFCC na bincike, Ortom

A wani labarin, Gwamna Samuel Ortom, ya ce baya tsoron hukumar EFCC kuma zai gabatar da kansa gareta idan ta kira shi.

Gwmanan na Benue ya ce a shirye yake hukumar ta bincike shi saboda ba shi ba wani shafaffe da mai bane kuma babu wani abu da yake boye wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel