Tinubu Bai Musluntar da Matarsa Ba Balle Ya Musluntar da Najeriya, Inji Kashim Shettima

Tinubu Bai Musluntar da Matarsa Ba Balle Ya Musluntar da Najeriya, Inji Kashim Shettima

  • An bukaci ‘yan Najeriya kan cewa kada su tada hankali game da cece-kuce da jita-jitan da ake na maida Najeriya daular Muslunci
  • Batun na fitowa ne daga bakin zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a ranar 27 ga watan Mayu
  • Ya bayyana cewa, mai gidansa Tinubu ya sha nuna daidaito tsakanin addinai, inda yace Tinubun ya auri mata fasto

FCT, AbujaZababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana matsayar gwamnatinsu da za a kafa game da maida Najeriya daular Muslunci.

Idan baku manta ba, Najeriya ta dauki dumi, musamman daga kiristoci a lokacin da Tinubu ya zabo Musulmi a matsayin abokin takara; Kashim Shettima.

An soki Tinubu ainun, inda kiristoci suka yi ta bayyana hango karshen siyasar sabin shugaban kasar a zaben 25 ga watan Faburairu.

Tinubu ba zai iya maida Najeriya kasar Muslunci ba, inji Shettima
Bola Ahmad Tinbubu da Kashim Shettima | Hoto: Bola Ahmad Tinubu
Asali: Facebook

Duk da haka, ya lashe zaben shugaban kasa na bana tare da samun kuri’u masu yawa da tazara tsakaninsa da ‘yan hamayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu bukatar sauya tsarin Najeriya

Da yake magana a taron lakca kan rantsar dasu, Shettima ya ce Najeriya bata bukatar wani sabon tashin-tashina, domin akwai abubuwa da yawa da gwamnatisnu za ta saka a gaba.

Ya fadi hakan ne a Abuja a yau Asabar 27 ga watan Mayu, inda ya bayyana kadan daga abubuwan da suka sanya a gaba.

Ya kuma shaida cewa, mai gidansa Tinubu yana mutunta dukkan addinai, don haka ne ma ya auri mata Kirista, kuma fasto a cocin RCCG.

Irin rayuwar Tinubu da ahalinsa

A cewarsa, kamar yadda muka gani a gidan talabijin na Channels:

“Ni da ne na lalura, babu ajandar maida Najeriya kasar Muslunci. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dai Musulmi ne da ya auri Kirista, ba ma gama garin Kirista ba fasto a cocin RCCG.

“Mutumin da bai Musluntar da ahalinsa ba, mutane na ta damuwa wai yana da niyyar maida Najeriya daula Islamiyya.”

Kiristoci sun ba ni kariya – inji Kashim Shettima

Da yake ci gaba da bayani, ya bayyana cewa, shugaban masu ba shi tsaro da kansa Kirista ne kuma tsaronsa a hannunsa yake.

Ya kuma bayyana cewa, ya yi hakan ne don tabbatarwa ‘yan kasa cewa, tabbas babu niyyar maida Najeriya daular Muslunci kamar yadda ke riritawa.

Ya zuwa yanzu, saura kasa da sa’o’i 48 a rantsar da Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shettima a ranar 29 ga watan Mayu.

Buhari: Shekaru 8 muka yi muna ceto yara daga hannun ‘yan bindiga

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, ya shafe shekaru takwas yana aikin tabbatar da tsaro a Najeriya.

Ya bayyana cewa, a cikin shekarun, gwamnatinsa ta ceto yara da yawa da ‘yan bindiga suka sace.

Ana yawan samun lokutan da tsagerun ‘yan bindiga ke sace dalibai a makarantu tare da neman kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel