May 29: Malami, Emefiele Da Sauran Yan Gwamnatin Buhari Da Tinubu Ba Zai Iya Aiki Da Su Ba

May 29: Malami, Emefiele Da Sauran Yan Gwamnatin Buhari Da Tinubu Ba Zai Iya Aiki Da Su Ba

Ana iya jin wasu daga cikin yan majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari shiru da zaran haifaffan janar din dan Daura ya mika mulki ga Bola Tinubu, zababben shugaban kasa a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Mambobin majalisar da suka hada da ministoci da sauran masu rike da mukamai na iya rasa shahararsu bayan mika mulki saboda irin sunan da suka siyawa kansu yayin da kuje mulki.

Shugaban kasa Buhari, Bola Tinubu da wasu manyan gwamnati
May 29: Malami, Emefiele Da Sauran Yan Gwamnatin Buhari Da Tinubu Ba Zai Iya Aiki Da Su Ba Hoto: Femi Adesina, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Wani dalili shine yadda suka buga wasansu gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ma babban zaben gaba daya.

Ga jerin wasu daga cikin yan majalisan a kasa:

Garba Shehu

Koda dai Shehu dan jarida ne, ana iya daina jin sunansa bayan barin mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

May 29: Jerin Yan Gwamnatin Buhari Da Tinubu Ka Iya Ci Gaba Da Tafiya Da Su Da Dalili

Wasu daga cikin dalilan da ka iya aiki a kansa shine ganin cewa har yanzu ana yi masa kallon mai kare Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma shirun da ya yi a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.

Godwin Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) yana daya daga cikin yan majalisar Buhari da za a iya jinsu shiru idan shugaban kasar ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai kuma, akwai yiwuwar gwamnati mai zuwa za ta binciki Emefiele kuma ba lallai ne ya kai labari ba saboda manufar sauya kudi da ya gabatar da shi yan kwanaki kafin zaben. Yana iya shahara saboda bincike da tuhumar da za a yi masa.

Yan siyasa da masana harkokin siyasa da dama sun ce gwamnan na CBN ya sauya kudin ne don bata damar da Tinubu ke da shi na zama shugaban kasa, sai dai abun takaici alamu sun nuna Emefiele ya dakatar da manufar sannan an daina ganin sabbin kudin sosai a kasar.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Kadarorinsa, Ya Ce Babu Wanda Zai Tsira a Mukarrabansa Bai Bayyana Nashi Ba

Abubakar Malami

Ba za a iya kiran Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a a matsayin babban dan siyasa ba duk da yana rike da mukami mafi girma a gwamnatin Buhari.

Ba lallai ne Tinubu ya baiwa Malami kowani mukami ba saboda zababben shugaban kasar zai fi son mutanen da za su kawo kuri'u kuma wanda ya daga darajar wanda ya dauke shi aiki.

Ana iya kallon Malami a matsayin dan siyasa mai rauni saboda ya ki yin murabus tare da gwada shahararsa a zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Kebbi gabannin zaben 2023, sabanin takwaransa, Timipre Sylva wanda ya yi murabus sannan ya yi takarar tikitin APC a Bayelsa kuma ya ci.

Chris Ngige

Ana iya jin ministan kwadago da daukar ma'aikata shiru bayan ya bar mulki saboda rashin goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC gabannin babban zabe da kuma gazawarsa wajen magance takkadamar da suka kunno kai karkashin kulawarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kashim Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Gaskiyar Zancen Abin da Zai Faru a Mulkinsu

A kwanan nan ne Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago na Najeriya ya ce ministan ya gaza magance takkadamar kasuwanci da dama sannan ya barwa gwamnatin Tinubu mai zuwa.

Adamu Adamu

Ministan ilimi mai barin gado na daya daga cikin ministoci mafi shahara a gwamnatin Buhari saboda yawan yajin aiki da makarantun jami'a suka tafi a cikin shekaru takwas da ya yi yana jagorantar ma'aikatan ilimin.

Abun takaici, ministan ya ragewa kansa girma ta hanyar cewa bai shirya ma mukamin ba kuma cewa shi sabon shiga ne a ma'aikatar lokacin da aka nada shi a matsayin minista.

Fashola, Ahmad da wasu yan gwamnatin Buhari da ka iya samun shiga gwamnatin Tinubu

Legit.ng ta rahoto a baya cewa za a rantsar da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar karagar mulki.

Ana ganin Tinubu zai yi tafiyarsa da wasu daga cikin yan majalisar shugaban kasa mai barin gado saboda biyayyarsu a gare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel