Gwamnan Jihar Yobe Ya Yiwa Fursunoni 115 Afuwa a Rana Daya, Ya Fadi Manufar Hakan

Gwamnan Jihar Yobe Ya Yiwa Fursunoni 115 Afuwa a Rana Daya, Ya Fadi Manufar Hakan

  • Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana ‘yantar da wasu fursunoni 115 da ke garkame a gidajen yarin jihar da ke Arewa maso Gabas
  • Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana manufar wannan afuwa da kuma shawarin da yake bayarwa game da ‘yantar da fursunoni
  • Ya kuma yabawa kwamitin da ya jagoranci aikin tabbatar da an tantance fursunonin da suka dace tare da ‘yanta su

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi afuwa ga fursunoni 115 da aka zabo daga cibiyoyin gyaran hali daban-daban a fadin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Afuwar ta biyo bayan nazarin da kwamitin da aka kafa yafiya karkashin jagorancin tsohon babban lauyan gwamnati kuma babban mai taimakawa gwamna na musamman kan harkokin shari’a Barista Sale Samanja ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Gabatar da Muhimmiyar Buƙata Ga Gwamnatin Tarayya Ana Gab da Rantsar da Tinubu

Da yake gabatar da rahoton, Samanja ya ce afuwar da gwamnan ta yi ya yi daidai da tanadin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yiwa kwaskwatima.

Jihar Yobe: An yafewa fursunoni 115
Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya | Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Barista Samanja ya ce duk wadanda aka sako din sun yi farin ciki da wannan karamcin da gwamnan ya yi musu, sun kuma yi alkawarin amfani da ‘yancin da suka samu wajen gyara kura-kuran da suka yi a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manufar ‘yanta fursunonin da ke garkame a Yobe

Da yake karbar rahoton kwamatin a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana rahoton afuwa ga fursunonin a matsayin muhimmin abin lura da kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an rage cunkoso a gidajen gyaran hali.

Buni ya ce a matsayinsa na gwamna, ya yi imani da matakan da za su saukaka gyaran halin fursunonin, yana mai kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wajen warware kananan tarar da ke jefa da dama cikin gidajen yari.

Kara karanta wannan

Yaron Kwankwaso Ya Yi Aikin, Shiyasa Aka Gayyace Shi Ya Bude – Gwamna El-Rufai

Gwamnan ya bayyana fatan cewa wadanda aka sako din sun koyi darasi ainun kuma za su kaucewa maimaita abin da ya jefa su gidan yari, DailyPost ta tattaro.

Ya yabawa kwamitin bisa kokarin da suka yi wanda ya kai ga samun nasarar tantance fursunonin 115 da suka dace tare da ‘yanta su.

Ganduje ya yi nadi dab da sauka daga mulki

A wani labarin, kunji yadda gwamnan jihar Kano ya yi sabon nadi yayin da ya saura masa kasa da kwanaki uku domin sauka daga mulki.

A cewar majiya, gwamnan ya rantsar da sabon kwamishinan hukumar zabe ne a daidai lokacin da ake jiran rantsar da sabon gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel