Yaron Kwankwaso Ya Yi Aikin, Shiyasa Aka Gayyace Shi Ya Bude – Gwamna El-Rufai

Yaron Kwankwaso Ya Yi Aikin, Shiyasa Aka Gayyace Shi Ya Bude – Gwamna El-Rufai

  • Nasir El-Rufai ya bayyana hikimar gayyato Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da ayyuka a Kaduna
  • Gwamnan mai barin-gadoya ce kamfanin da ya samu kwangilar kasuwar U/Rimi 'Dan tsohon Gwamnan Kano ne
  • Malam El-Rufai ya kira manyan ‘yan siyasar kasar nan zuwa wajen bude wasu ayyukan da ya yi a gwamnatinsa

Kaduna - Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu ayyuka da ya yi.

Da yake jawabi wajen bude kasuwar Unguwar Rimi da wasu tituna da aka gina, Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin gayyato tsohon Gwamnan na Kano.

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samu, an ji Malam El-Rufai ya na cewa gwamnatinsa ba ta gina kasuwanni, ta bar wannan ga ‘yan kasuwa.

Kwankwaso da El-Rufai
Rabiu Kwankwaso a Kaduna Hoto: Hon. Saifullahi Hassan @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A irin haka ne gwamnati mai barin-gado ta tallata kwangilar sake gina tsohuwar kasuwar da ke Unguwar Rimi wanda tayi shekara da shekaru a haka.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: El-Rufai Ya Tsige Magatakardar majalisar Jihar Kaduna Da Wasu 2

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

El-Rufai ya ce da aka tashi zakulo wanda zai yi aikin, sai aka yi dace wani matashi ya yi nasara.

Wanene matashin nan?

Abin da ya ba mutane mamaki shi ne da Gwamnan ya ce wani daga cikin yaron tsohon Gwamnan na jihar Kano ne ya mallaki kamfanin da ya yi aikin.

A cewar Malam El-Rufai, shiyasa su ka kira Sanata Kwankwaso ya zo domin ganin kokarin da yaron cikinsa ya yi kamar yadda ya saba a wasu wuraren.

"Ba mu sa kudin gwamnati wajen gina kasuwanni sai idan akwai matukar bukatar domin kasuwanni hanyar samun kudi ne
Kamfanoni ne su ke yi, saboda haka mu ka tallata kuma mu ka samu wani ‘dan kasuwa – Kamfanin Piyo Global na wani matashi
Matashin ya yi irin wadannan ayyuka na gine-gine a Kaduna, sai kuma aka yi sa’a ya zama yaron Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Gayyaci Kwankwaso Kaddamar Da Ayyukan Karshe Da Ya Yi A Kaduna

Shiyasa mu ka ga bukatar mu gayyaci Mai girma Sanata (Kwankwaso) ya bude wannan aiki, ya ga yadda yaronsa ya yi nisa
Sai ya san cewa watakila lokaci ya yi da zai matsa gefe, ya bar wa wannan yaro mai matukar kokari.

- Nasir El-Rufai

Daga Neja sai Kaduna

A karo na biyu a cikin kwanaki biyu, an ji labari wani Gwamnan APC ya gayyato jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jiharsa

Kafin Nasir El-Rufai ya bar mulki, an ji ya kira tsohon Gwamnan Kano ya kaddamar da ayyukan da ya yi, a mako mai zuwa Gwamnan zai sauka daga karaga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel