Malami Ya Bayyana Gaban Kwamitin Majalisa Kan Ɓacewar Dala Biliyan 2.4 Na Ɗanyen Mai

Malami Ya Bayyana Gaban Kwamitin Majalisa Kan Ɓacewar Dala Biliyan 2.4 Na Ɗanyen Mai

  • Atoni Janar na Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami ya ce ofishinsa ya yi nasarar dawo da $1bn na danyen mai
  • Abubakar Malami ya bayyana haka ne yayin da yake bayani game da bacewar wasu kudade na gangar danyen mai
  • Wannan shi ne karo na biyu da Atoni din ya ke bayyana a gaban kwamitin bincike don sanin yadda wasu kudade suka makale

FCT, Abuja - Atoni Janar na Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami ya bayyana cewa a halin yanzu ofishinsa ya yi nasarar samo fiye da $1bn ga kasar Najeriya.

Malami ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai da aka kafa don bincike inda $2.4bn suka makale daga kudin shiga na gangar danyen mai 48m a shekarar 2015.

Atoni Janar, Abubakar Malami
Atoni Janar Ya Bayyana Gaban Kwamitin Majalisa. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Gidan talabijin na Channels ta tattaro cewa wannan shi ne karo na biyu da Atoni din ya bayyana a gaban kwamiti din majalisar.

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Ya bayyana matsayarsa ta farko da cewa bai san bayanai game da bacewar kudaden ba da kuma martaninsa ga kwamitin akan bayanai na dawo da kudaden tun shekarar 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta bayyana cewa bangarorin biyu sun gagara samun fahimtar juna akan bayanai game da asusun bai daya na gwamnatin tarayya da aka bayyana a cikin kundin tsarin mulki.

Malami ya yi alkawarin taimaka wa kwamitin

Duk da cewa gwamnati mai ci ta shugaba Buhari da ita kanta majalaisar ta 10 suna kokarin kammala wa’adinsu, Atoni Janar din ya amince ya yi aiki kafada da kafada da kwamiti din don sanin tushen yadda aka yi kudaden suka bace.

Emefeile da Zainab Ahmed ba su zo gaban kwamitin ba don bincike

Har ila yau, ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed da gwamnan babban bankin Najeria (CBN), Godwin Emefiele ba su zo gaban kwamiti din ba don samun bayanai da za su taimaka wurin sanin yadda kudaden suka bace.

Kara karanta wannan

Nasarar Tinubu: Allah Ne Ya Karbi Addu’ar Mu Na Neman Wakilci Na Gari, Sanata Kabiru Gaya

Afuwa ga Barayi: Ana binciken Hadiman Abubakar Malami kan ‘karbar kudi’

A wani labarin, Hukumar EFCC ta tsare wasu daga cikin manyan jami’an ma’aikatar shari’a bisa zargin karban makudan kudade.

Rahotanni sun tabbatar cewa ana zargin mutanen ne da karban kudi don yi wa barayi afuwa.

Wata majiya ta ce hadiman ministan shari'a Abubakar Malami suna tattara sunyen mutanen da za a yi wa afuwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel