Nasarar Tinubu: Allah Ne Ya Karbi Addu’ar Mu Na Neman Wakilci Na Gari, Sanata Kabiru Gaya

Nasarar Tinubu: Allah Ne Ya Karbi Addu’ar Mu Na Neman Wakilci Na Gari, Sanata Kabiru Gaya

  • Sanata Kabiru Gaya ya bayyana nasarar Tinubu da cewa addu’ar ‘yan Najeriya ne ta karbu na neman waklici nagari
  • Sanatan ya bayyana haka ne a Abuja ga manema labarai inda ya ce Tinubu da Shettima sun dace da kasar Najeriya
  • Ya bayyana kwarin guiwar cewa wannan hadakar za ta kawo ci gaba a Najeriya duba da tarihinsu na baya

Jihar Kano – Sanata Kabiru Gaya ya bayyana nasarar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da cewa Allah ne ya amsa addu’ar ‘yan Najeriya na samun wakilci na gari.

Sanatan ya bayyana haka ne ga manama labarai yayin taron addu’o’i wanda masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta shirya, don samun kariya da ci gaba ga gwamnati mai zuwa.

Sanata Kabiru Gaya mai wakiltar Jihar Kano
Sanata Kabiru Gaya na Kano ya ce Allah ya amsa addu'arsu ya basu Tinubu. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Sanata Gaya wanda ke wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa ya ce lokacin da Tinubu yake gwamnan Lagos kowa ya ga irin ayyukan alkairi da ya yi.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Gaya ya bayyana kwarin guiwarsa ta samun ci gaba a kasar

Ya bayyana kwarin guiwarsa da cewa Tinubu zai yi fiye da abin da ya yi lokacin da yake gwamnan Lagos wurin kawo abubuwan ci gaba da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa mataimakinsa, Kashim Shettima shima ya yi kokari sosai lokacin da yake gwamnan jihar Borno wurin dakile rashin tsaro da ya addabi jihar, Tribune ta tattaro.

Hadakar Tinubu da Shettima ba karamar nasara ba ce

Rahotanni sun tattaro Gaya yana cewa tabbas hadakar Tinubu da Shettima zai kawo wa Najeriya ci gaba wanda za ta zamo abin koyi ga wasu kasashe.

A cewarsa:

“Ina da tabbacin cewa Allah zai taimake su wurin zakulo kwararru da za su rike mukamai a gwamnati daban-daban kuma su kawo ci gaba ga mutanen Najeriya.”

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Ganduje ya yi karin haske kan faifan muryarsa da ke yawo na sukar Tinubu

Za a rantsar da Bola Tinubu a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, wadda zai bude sabon shafi na shekara hudun farko.

Sarakunan Gargajiya Sun Bukaci Tinubu Ya Dawo Da Matsayin Masarautu a Kundin Tsarin Mulki

A wani labarin, kungiyar sarakunan Yarbawa ta Yoruba Obas Forum sun bukaci Bola Tinubu ya dawo da martabar sarakuna cikin kundin tsarin mulki.

Kungiyar wadda ta kunshi manyan sarakuna a yankin Kudu maso Yamma sun bayyana cewa matakin zai kawo zaman lafiya a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel