Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa shi mutum ne mai saurin fushi, amma baya kwana da kowa a ransa
  • Zulum ya bayyana hakan ne yau Alhamis a yayin taron bankwana da ya yi da 'yan majalisar zartarwar jihar ta Borno
  • Ya godewa kwamishinoninsa da sauran muƙarabban gwamnati bisa irin gudunmawar da suka ba gwamnatinsa ta cimma nasarorin da ta samu

Maiduguri - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce duk da cewa yana da saurin fushi, ba ya kwanciya da fushin kowa a ransa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake neman yafiyar mambobin majalisar zartarwarsa a zaman da aka yi a Maiduguri, ranar Alhamis.

Zulum ya ce ba ya rike kowa a ransa duk da zafin ransa
Zulum ya ce ba ya rike kowa a ransa duk da zafin ransa. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya bayyana cewa mutane da dama za su riƙa kallonsa a matsayin mutum mai saurin fushi, sai dai ya ce baya kwanciya barci da fushin kowa a ransa, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

A cewar Zulum:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Eh, da yawa daga cikinku za su ce ni mutum ne mai zafin rai, wannan dabi'ata ce, amma kuma, ba na kwanciya barci da wani a cikin rai na."

Zulum ya fuskanci ƙalubale babba

Zulum ya ce bai taɓa samun irin ƙalubalen da ya samu ba a tsakankanin shekarun 2019, 2020 da 2021 wanda yake aiki cikin yanayi mara tabbas, na yaƙi da kungiyar Boko Haram.

Zulum ya kuma ƙara da cewa a cikin shekaru huɗun da suka gabata, sun sami damar yi wa al'ummar jihar Borno ayyuka da dama ba tare da wani kokwanto ba.

Ya ce duk da kasancewarsa ɗan adam ajizi, ya tabbatar da cewa abubuwan da gwamnatinsa ta yi a tsawon wannan lokaci, abubuwa ne da jama'a suka yaba.

A kalamansa:

“Mun yi aiki tuƙuru domin amfanin al’ummar jihar Borno a cikin shekaru huɗu da suka gabata ba tare da wani kokwanto ba.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

"Mu mutane ne kuma ba mu cika ɗari bisa ɗari ba, amma duk da kasawarmu, na yi imani mun yi aiki da kyau."

Zulum ya godewa kwamishinoninsa

Ya nuna matukar godiya ga ɗaukacin ‘yan majalisarsa kan yadda suka taimaka wajen yin ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar.

Ya bayyana cewa duk wasu nasarori da gwamnatinsa ta samu, ta samesu ne ta dalilin goyon baya da kuma jajircewarsu wajen aiwatar da ayyukan da aka sanya su.

Zulum ya ce:

“Gwamnatina ba za ta cimma abubuwan da ta cimmawa ba, in ba tare da gudummawarku ga manufofina da kuma kuɗurorina ga jihar ba. Da ba za mu cimma hakan ba, in ba don jajircewarku ba.”

Jaridar vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa da kuma sauran mukaman gwamnati a wurin taron.

Buhari ya bai wa Zulum N15bn don gina wasu ƙauyuka

A wani labarin namu na baya, kun karanta cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa gwamnan jihar Borno zunzurutun kuɗi har N15bn domin sake gina wasu ƙauyuka.

Zulum dai ya sha alwashin sake gina wasu ƙauyuka da 'yan ta'addan Boko Haram suka lalata domin bai wa 'yan gudun hijira damar dawowa garuruwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel