FEC: Sunayen Kwamishinonin RMFAC 7 da Aka Rantsar a Taron Karshe a Mulkin Buhari

FEC: Sunayen Kwamishinonin RMFAC 7 da Aka Rantsar a Taron Karshe a Mulkin Buhari

  • Muhammed Buhari ya tabbatar da nadin Kwamishinoni bakwai da za su yi aiki a Hukumar RMFAC
  • Shugaban Najeriya mai barin-gado ya rantsar da su ne a taron FEC na karshe da aka yi a Aso Rock
  • A cikin Kwamishinonin akwai tsohon Sanatan Arewacin Enugu a Majalisar Dattawa, Ayogu Eze

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammed Buhari ya rantsar da Kwamishononin tarayya a hukumar RMAFC mai alhakin yanka albashi a Najeriya.

An rantsar da sababbin Kwamishononin ne a taron majalisar FEC na karshe da za ayi a gwamnatin Muhammadu Buhari, The Cable ta kawo rahoton.

Jim kadan bayan rantsar da Kwamishononi sai mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya gabatar da rahoton kwamitin gyara kiwon lafiya.

Kwamishinonin RMFAC
Taron FEC a Abuja Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Kwamitin da Farfesa Osinbajo ya jagorantar domin kawo gyara a harkar lafiya ya bada shawarar a kara kudin da ake kashewa domin kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Yin Nadin Sababbin Mukamai Ana Saura Kwana 6 a Rantsar da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce wadannan Kwamishinoni sun fito ne daga Kudu da Arewacin jihohin kasar nan.

A nadin da aka yi, Legit.ng Hausa ta fahimci Arewa maso gabas da Kudu maso kudu ba su da wakilci, an samu maza biyar, akwai mata biyu.

1. Mr Peter Okpara – Jihar Imo

2. Sanata Ayogu Eze - Jihar Enugu

3. Kolade Abimbola - Jihar Oyo

4. Rekiya Ayuba-Haruna – Jihar Kebbi

5. Hauwa Aliyu – Jihar Jigawa

6. Ismaila Agaka - Jihar Kwara da

7. Ambasada Ayuba Ngako – Babban birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Kowane Minista ya halarta

Jaridar The Nation ta ce taron da aka yi na yau a Aso Rock wanda shi ne na karshe, ya cika ya batse.

Kowane Minista ya samu halartar zaman majalisar Ministocin tarayyan, bayan taron ne Ministoci za su ajiye mukamansu, su jira sabuwar gwamnati.

Kara karanta wannan

Manyan Abubuwa 7 Da Suka Faru Tsakanin 2019 da 2023 a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya

An yi Darekta a NDPHCL

Rahoton da aka fitar a baya ya nuna Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Steven Andzenge a matsayin Darekta a NDPHCL.

Dr. Steven Andzenge MON ya zama Darektan shari’a/Sakataren kamfanin NDPHCL. Zai fara yin wa’adin shekaru hudu a ofis, zai bar kujerar a 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel