Buhari Ya Sake Yin Nadin Sababbin Mukamai Ana Saura Kwana 6 a Rantsar da Tinubu

Buhari Ya Sake Yin Nadin Sababbin Mukamai Ana Saura Kwana 6 a Rantsar da Tinubu

  • Sanarwa ta fito cewa Kamfanin wutar lantarki a Najeriya na NDPHCL ya samu sabon Darekta
  • SGF ya ce Mai girma Muhammadu Buhari ya amince Dr. Steven Andzenge ya zama Darekta a kamfanin
  • Ana cigaba da nadin mukamai duk da a farkon makon gobe za a rantsar da sabon shugaban Najeriya

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Steven Andzenge a matsayin Babban Darekta a NDPHCL.

A ranar Talata ne The Nation ta kawo rahoto cewa Dr. Steven Andzenge zai rike kujerar Darekta na bangaren shari’a na kamfanin.

Kamar yadda sanarwar da aka fitar ta tabbatar, sabon Darektan zai kasance Sakataren NDPHCL daga yanzu zuwa Mayun 2027.

Shugaba Buhari
Muhammadu Buhari a ofis Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Sanarwar ta fito ne a Abuja daga bakin Darektan yada labarai a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey a makon nan.

Kara karanta wannan

Zaman da Kwankwaso Ya Yi da Tinubu a Faransa Zai Iya Canza Siyasar APC da Majalisa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Willie Bassey ya ce wa’adin sabon Darektan ya fara ne daga ranar 16 ga watan Mayun nan, kuma zai fara yin shekaru hudu a ofis.

Jawabin da OSGF ya fitar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr. Steven Andzenge MON a matsayin Darektan shari’a/Sakataren kamfanin NDPHCL.
Zai fara yin wa’adin shekaru hudu a ofis da za su soma aiki daga ranar 16 ga watan Mayun 2023.

- Willie Bassey

Mukaman da Andzenge ya rike

Jaridar Sun ta ce kafin samun wannan mukami, sabon Darektan ya rike kujerar babban Kwamishina a hukumar NERC mai kula da wuta.

Bayan aiki da ya yi da hukumar kula da harkokin wuta, Andzenge ne shugaban kwamitin shugaban kasa da aka tura zuwa jami’ar UDUS.

Mai girma shugaban Najeriya ya taya shi murnar samun wannan mukami, sannan ya yi kira gare shi da ya nuna irin kwarewar da yake da ita.

Kara karanta wannan

Saura Kwanaki 6 a Bar Aso Rock, Hanan Tayi Magana a Kan Mulkin Shugaba Buhari

Nade-nade a ma'aikatar jirgin sama

A makon nan ne aka samu labari Kabir Mohammed ya zama sabon shugaban FAAN, sannan Tayib Odunowo ya karbi rikon hukumar NAMA.

Baya ga Darektoci da aka nada a hukumomin FAAN, NCAA, NIMET, NSIB da NAMA, an tsawaita wa’adin Alkali Moddibo a makarantar NCAT.

Philip Agbese ya koka

An samu rahoto zababben 'dan majalisar tarayya, Philip Agbese yana so Gwamnatin da za ta karbi mulki tayi bincike kan Muhammadu Buhari.

A mako daya, Shugaban kasa ya raba mukamai fiye da 10 a Najeriya, Agbese ya ce garajen da ake yi wajen nade-naden ya nuna da walakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel