Yadda Daura ke Shirin Tarbar Shugaba Buhari Bayan Bayajidda II Ya Sauka Daga Mulki

Yadda Daura ke Shirin Tarbar Shugaba Buhari Bayan Bayajidda II Ya Sauka Daga Mulki

  • Shirye-shirye ake yi na musamman domin ayi wa Muhammadu Buhari lale maraba a garin Daura
  • Shugaba mai barin-gado zai tare a mahaifarsa bayan sauka daga karagar mulki nan da 'yan kwanaki
  • Za ayi bukukuwa da wasanni da nufin karramar Buhari wanda ya yi shekaru takwas ya na mulki

Katsina - Mutanen garin Daura su na shirin yin biki mai kamar sallah domin yin maraba ga Muhammadu Buhari wanda zai sauka daga kan mulki.

A rahoton da Daily Trust ta fitar, an fahimci Mai martaba Sarkin Daura, Dr. Umar Farouq Umar ne kai gaba a shirye-shiryen tarbar Muhammadu Buhari.

An fahimci Mai martaba da kan shi yake kai ziyara zuwa wurare domin ganin yadda ayyukan yi wa shugaba mai barin-gado lale maraba su ke ta gudana.

Buhari Daura
Shugaban kasa a Daura Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wata majiya a fadar Daura ta ce Sarki Umar Farouq Umar ya ba lamarin matukar muhimmanci.

Kara karanta wannan

Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masarautar Daura ta na shirya gagarumar hawa, wasan dambe, kokowa da sharo da za ayi domin karrama Muhammadu Buhari wanda shi ne Bayajidda II.

Sarkin Daura ya shaidawa Gwamna Aminu Bello Masari shirin hawan da ake yi a lokacin da ya ziyarci Mai martaba a fadarsa, har ya ba shi goron gayyata.

Rahoton ya ce kungiyoyi da dinbin mutane da-dama za su yi wa shugaban na Najeriya lale, su yi masa rakiya zuwa gidansa da zarar ya shigo garin.

Shugaban kungiyar DEDA, Alhaji Aliyu Daura ya ce za su saurari Buhari tun daga kauyen Dannakola, manya za su bi shi filin jirgin sama da ke Katsina.

Hawa na musamman

Daga safiyar 30 ga watan Mayun 2023 za a fara hawan a filin Kangiwa da ke birnin Daura. Hakimai da masu gari za su hallara ne a kofar Sarki Abdurrahman.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Vanguard ta ce Daurawa na murna da cigaba da suka samu na makarantu, asibitoci da abubuwan more rayuwa a tsawon shekarun da ‘dansu ya yi a kan mulki.

Baya ga hawan da za a shirya, an tabbata an gyara gidan Muhammadu Buhari da yake Daura. Haka zalika ana gyare-gyare a gidansa da ya ke jihar Kaduna.

An yi wa gidan farin fenti duk da jami’an tsaro ba su bari a shiga ko a iya daukar hoto, sai da baya ga fentin, babu wani canjin bada labari da gidan ya samu.

Ayyukan Gwamnatin APC a kasa

A karkashin mulkinsa, an ji labari Muhammadu Buhari ya gina hanyoyin kilomita 9,290.34, sannan an daura alamu 254,690 a kan titunan tarayya da ake da su.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya ce sun amince a gina ko a gyara tituna 155 kuma ana gina gidaje 6, 000 a fadin jihohi da birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel