Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

  • Gwamnan jihar Jigawa ya karyata zargin cin dunduniyar zababben Gwamna, Mal. Umar Namadi
  • Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce wasu munafukai ne ke neman haddasa masu fitina a APC
  • Gwamna mai shirin barin-mulki ya yi karin-haske yayin da ya zauna da jigon AP, Isa Ahmad Gerawa

Jigawa - Mai girma Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatar da cewa bai da wani nufi na yakar gwamnatin Malam Umar Namadi da za ta gaje shi.

Daily Trust ta ce Muhammad Badaru Abubakar ya yi wannan bayani ne a lokacin da Alhaji Ahmad Isa Gerawa ya kai masa ziyara a gidan gwamnati.

Ganin rade-radi sun fara yawa cewa gwamnan Jihar Jigawa ya shiryawa magajinsa gadar-zare, Gwamna Badaru Abubakar ya fito ya wanke kan shi.

Gwamnan APC da Gwamna Mai Jiran Gado
Gwamna Badaru Abubakar da Umar Namadi wajen kamfe Hoto: O. C. Sankara
Asali: Facebook

Gwamnan mai barin-gado ya ce wasu fusatattun munafukai da su ka rasa gindin zama a jam’iyyar APC ne suka ta yada wannan jita-jita a Jigawa.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma Don Gina Gidaje a Dubai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce Badaru Abubakar ya tabbatar da cewa har da wasu abokansa a siyasa da ‘yan gaba-gaba a jam’iyyarsu ta APC wajen jifansa da sharrin.

Gwamnan ya ke cewa masu yin hakan ba su da wata manufa illa su jawo rudani saboda burinsu, a dalilin haka ya ja-kunnesu da su guji wannan aiki.

“Abin takaici ne mu na rufe kofofi, mu yi zama da makiyanmu, mu na tattauna tsare-tsaren gwamnati; yadda za mu kawo cigaba a jihar Jigawa.
Abin da ba mu sani ba shi ne, ashe ba tare su ke da mu ba. Mafi yawan wadannan bakaken ashana su na hassadar nasarorin da mu ka samu a mulki ne.
Sun zama munafukai, su na yada karyayyaki, su na gulma, wanda hakan ya jawo sabani tsakanina da wasu shugabanni jam’iyya da jami’an gwamnati.”

Kara karanta wannan

Yadda Aka Ji Ganduje a Tarho Yana Kokawa Kan Zaman Tinubu da Kwankwaso a Faransa

- Muhammad Badaru Abubakar

An nemi afuwar juna

Leadership ta rahoto Alhaji Isa Ahmad Gerawa yana saura kiris rikici ya barke a jam’iyyar APC, a cewarsa hakurin Badaru ya jawo aka zauna lafiya.

Shugaban kamfanin Gerawa Globacom ya soki masu haddasa fitina, ya ce sun yafewa Gwamna mai barin-mulki, kuma su na fatan zai yafe masu.

Rabiu Kwankwaso a Legas

A rahoton da mu ka fitar a baya, an samu bayanai a kan abin da ya kai jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf zuwa jihar Legas.

Rabiu Musa Kwankwaso da zababben Gwamnan za su je wajen kaddamar katafaren matatar da Aliko Dangote wanda shugaban kasa zai bude a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel