Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

  • Kusan mako daya ya rage a rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a kan kujerar shugaban kasa
  • Masana sun yi bayanin wasu bangarorin da ya kamata gwamnati mai zuwa ta dage sosai a kan su
  • Akwai ayyuka da-dama da ba a karasa ba da tulin bashi da Muhammadu Buhari zai bari ga magajinsa

A ranar Litinin, jaridar Daily Trust ta tattaro wadannan bangarori kamar haka:

1. Tsaro da fafutukar raba kasa

Dole gwamnatin Bola Tinubu ta kawo karshen garkuwa da mutane, fasa bututun danyen mai, rikicin makiyaya da kuma masu neman a barka Najeriya.

A kowane yanki ana fama da matsalar tsaro, shiyasa ake ganin akwai bukatar a nemi hadin-kan sarakuna, masana da majalisa domin zaman lafiya.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

To Fah: Kwankwaso, Wike da Wasu Yan Adawa 4 da Ka Iya Shiga a Dama Dasu a Mulkin Tinubu

2. Lantarki da tallafin fetur

A yanzu akwai sarkakiya a sha’anin wutar lantarki, za a ga yadda Tinubu zai magance yadda DisCos suke aiki tare da inganta karfin wutan da ake samu.

Wani bangare shi ne tallafin fetur inda tsarin yake cinyewa gwamnati kudin shiga, tashin farashin kuma zai jawo karin tashin farashin kaya a Najeriya.

3. Noma da abinci

Irinsu shugaban kungiyar manoma ta AFAN sun fara bada shawarar a dage wajen noma abinci a ko yaushe a shekara tare da rungumar fasahar zamani a noma.

Rahoton ya ce ana bukatar a saukakawa manoma domin kayan abinci su yi sauki. Muhammadu Buhari ya rufe iyakokin kasa saboda a noma abinci a gida.

4. Kiwon lafiya

Har zuwa ‘yan kwanakin nan, manyan likitoci sun yi yajin-aiki a Najeriya. Manyan mutane su na fita kasashen ketare, su kan su ma’aikatan su na barin gida.

Dr. Abubakar Muhammad Tanko Likita ne a jihar Kaduna, ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa abubuwa kusan uku suke jawo likitoci ke barin Najeriya.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Bai Kamata Shugaban Kasa Ya Sake Fita Kasashen Waje Don Neman Magani Ba

Likitan ya ce na farko albashi ya yi kadan, sannan aiki ya yi wa malaman asibiti yawa saboda barin aiki da ake yi, sannan babu isassun kayan yin aiki.

5. Ilmi

Kamar yadda ake fama da matsalar kiwon lafiya, mutane da-dama su na barin kasar nan domin su yi karatu a ketare, haka malamai su na ajiye ayyukan su.

Yajin-aikin kungiyar ASUU ya zama al’ada a duk bayan ‘yan watanni, baya ga kuka da ake yi a kan yadda ilmi ya tarbabare a kusan kowane mataki a yau.

6. Tattalin arziki da bashi

Zuwa yanzu, Tinubu ya na sane da zai gaji bashin Naira tiriliyan 77, wannan ya sa wasu masana ke ganin ya kamata Najeriya ta nemi a yafe mata kudin nan.

A bangaren tattalin arziki, ya zama wajibi gwamnati mai zuwa ta tara masanan da za su yi maganin hauhawar farashi, tabarbarewar darajar Naira da rashin aikin yi.

Kara karanta wannan

Kungiyar MURIC Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Kirista Dan Kudu a Shugabancin Majalisar Dattawa

7. Ayyuka da kwangiloli

Idan Tinubu ya shiga ofis, zai ci karo da manyan ayyuka da gwamnatin APC ba ta kammala ba, daga jirgin kasan Kano-Katsina-Jibiya-Maradi zuwa tituna.

Manyan kwangilolin da ke bukatar kula sun hada da jirgin Farakwal-Maiduguri, titin Abuja-Kano, dogon Kano-Kaduna, aikin AKK da na lantarkin Siemens.

Daura za ta yi wa Buhari lale

A gwamnatin Muhammadu Buhari, kun ji labari Daura ta samu jami’a, Polytechnic, asibitoci, tituna da ruwa da cigaban wutar lantarki da dogon jirgin kasa.

Saboda haka ne Sarki, Masarauta da ‘Yan gari za su shiryawa Buhari kyakkyawan tarba har da yin hawa da sharo domin yi wa ‘dansu maraba da dawowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel