Jerin Taro, Wasanni da Shagulgulan Mika Mulki 12 da Za a Shirya na Tsawon Kwana 7

Jerin Taro, Wasanni da Shagulgulan Mika Mulki 12 da Za a Shirya na Tsawon Kwana 7

  • An shirya taro da liyafa da bukukuwa dabam-dabam a shirye-shiryen rantsar da shugaban kasa
  • Boss Mustapha ya sanar da abubuwan da aka yi tanadi kafin Muhammadu Buhari ya mika mulki
  • Za a yi wadannan taro ne a Aso Rock, Masallacin kasa, Coci, Farfajiyar Eagle da sauran wurare

Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce akwai taro da liyafa da lacca da za a gabatar duk a cikin shirye-shiryen rantsar da shugaban kasa.

Premium Times ta ce za a dauki mako guda ana shagulgula a birnin Abuja.

Zababbun shugabanni su na samun mafi girmar lambar yabo, a 2010 ne aka saba ka’ida da Goodluck Jonathan ya hau mulki, za ayi irin haka a wannan karo.

Dr. Goodluck Jonathan ya samu mulki ne bayan rasuwar Ummaru Yar’Adua, sai majalisar koli ta ba shi lambar yabon da ya zama sabon shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Buhari
Janar Muhammadu Buhari a kayan Sojoji Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Talata 23 ga watan Mayu 2023

Liyafa da za a shirya domin karrama Shugaban kasa

A gidan sojoji da karfe 7:00 na dare.

Laraba 24 ga watan Mayu 2023

Wednesday, 24th May 2023

Taron majalisar FEC na karon karshe

A dakin taron majalisar a fadar shugaban kasa

Alhamis, 25 ga watan Mayu 2023

Karrama zababben shugaban kasa da mataimakinsa da lambobin girman GCFR da GCON da kuma mika takardun karbar gwamnati

A babban dakin taro na fadar shugaban kasa da karfe 10:00 na safe.

(Masu halarta za su zauna da karfe 9:00ns)

Juma’a, 26 ga watan Mayu 2023

Lacca ta musamman da sallar Juma’a

Babban masallaci da karfe 10:00ns da 1:30nr

Lacca a kan karfafa damukaradiyya wanda Mai girma tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru M. Kenyatta zai gabatar

A babban dakin taro na kasa da karfe 10:00ns

Kara karanta wannan

Yadda Sanatoci Za Su Gujewa Kuskuren da APC Ta Tafka a 2015 – Shugaban Jam’iyya

(Masu halarta za su zauna da karfe 9:00ns)

Asabar 27 ga watan Mayu 2023

Taron ranar yara

I. Fareti

II. Liyafar yara

A tsohon filin farteti da karfe 10:00ns

A dakin taron fadar shugaban kasa da karfe 2:00nr

Lahadi 28 ga watan Mayu 2023

Zaman coci

A babban cocin kasa da karfe10:00ns

Liyafar rantsuwa/Daren gala

Dakin taron fadar shugaban kasa 7:00ns

Litinin 29 ga watan Mayu 2023

Faretin rantsuwa/mika mulki

Farfajiyar Eagle Square, CBD da karfe10:00ns

Liyafar bayan rantsuwa

Fadar shugaban kasa da karfe 1:30 (za a shiryawa shugaban kasa, takwarorinsa da sauran shugabanni da wadanda aka gayyata).

Lambobin GCFR da GCON

Kafin Muhammadu Buhari ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, an ji labari zai bada lambar yabo ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa.

Baya ga lambar yabo na GCFR da GCON da Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima za su samu, Premium Times ta ce akwai abubuwa iri-iri da za ayi.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel