Buhari Zai Karrama Tinubu da Shettima da Lambar Yabo Ta Kasa Gabanin Rantsarwa

Buhari Zai Karrama Tinubu da Shettima da Lambar Yabo Ta Kasa Gabanin Rantsarwa

  • Shugaba Buhari zai karrama Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima kwanaki kaɗan gabanin wa'adin mulkinsa ya ƙare
  • A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasan ta fitar, za'a yi bikin karramawar ranar 25 ga watan Mayu, 2023
  • Haka nan idan Allah ya kaimu ranar 29 ga watan Mayu, Buhari zai sauka ya miƙa wa Tinubu mulki a hukumance

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da cewa ya shirya karrama zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Buhari ya bayyana cewa zai karrama sabbin shugabannin biyu da lambobin yabo na kasa gabanin su karbi ragamar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Tinubu, Buhari da Shettima.
Buhari Zai Karrama Tinubu da Shettima da Lambar Yabo Ta Kasa Gabanin Rantsarwa Hoto: ABAT, Buhari Sallau
Asali: Twitter

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin kafafen watsa labaran zamani, Tolu Ogunlesi, ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Ban Gane Ba," Atiku Ya Maida Martani Kan Kiran da Sakataren Amurka Ya Yi Wa Tinubu Ta Wayar Tarho

Ya ce shugaban kasa zai baiwa Tinubu da Shettima lambobin karramawar ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, kwanaki 4 gabanin su karɓi ragamar ƙasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane lambar karramawa Buhari zai baiwa Tinubu da Shettima?

Hadimin shugaban ƙasan ya ce za'a karrama Tinubu da lambar yabon GCFR (Grand Commander of the Order of the Federal Republic) yayin da Shettima zai samu lambar GCON (Grand Commander of the Order of Niger).

Ya ce bayan wannan karramawa, gwamnatin Buhari zata yi amfani da wannan dama ta miƙa takardun miƙa mulki ga Tinubu da Shettima duk a wannan rana.

A cewar sanarwan, wannan rana zata yi kyau kuma zata ƙayatar a tarihin Najeriya, sannan zata kara tabbatar da dokar zartaswa 14, wacce shugaban kasa Buhari ya rattaba wa hannu.

Sanarwan ta ce:

"A ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, 2023, Shugaba Buhari zai karrama zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima da lambobin GCFR da GCON bi da bi."

Kara karanta wannan

"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru

Bayan nan shugaba Muhammadu Buhari, zai miƙa ragamar mulkin Najeriya hannun zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 a hukumance.

Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Ganawarsa da Bola Tinubu a Faransa

A wani labarin kuma Jagoran NNPP mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso, ya ce tabbas ya sa labule da zababben shugaban masa a ƙasar Faransa.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce sun tattauna batutuwa da dama kuma ba sau ɗaya suka gana ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel