Kamar Taure: Da Zarar Mijina Ya Ga ‘Skirt’, Sai Tsuminsa Ya Tashi, Matar Aure Ta Fadawa Alkali a Kotu

Kamar Taure: Da Zarar Mijina Ya Ga ‘Skirt’, Sai Tsuminsa Ya Tashi, Matar Aure Ta Fadawa Alkali a Kotu

  • Wata mata mai suna Oluwatoyin Falade ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta saboda tsananin bin mata da yake
  • Oluwatoyin mai shekaru 44 ta ce sun shafe shekaru fiye da 11 suna zaune amma ta gaji da zama da shi
  • Mijin mai suna Segun ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa kuma ya yi alkawarin gyara halayensa

Jihar Lagos - Wata mata mai suna Oluwatoyin Falade a ranar Laraba ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta Segun saboda yawan neman mata da yake yi.

Oluwatoyin mai shekaru 44 ta ce sun shafe shekaru 11 suna zaman aure kuma Allah ya azurtasu da ‘ya’ya biyu da mijin nata.

kotu/matar aure
Mata Ta Koka Kan Yadda Mijinta Ke Bin Mata a Jihar Lagos. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Ma’auratan na rayuwa ne unguwar Tunde Davids dake Agege cikin jihar Lagos, cewar jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Ina Matukar Son Matata: Fasto Ya Roki Alkali Kada Ya Datse Igiyar Aurensa

A cewarta matar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mijina manemin mata ne duk inda ya hango mace, to hankalinsa zai karkata gare ta.
“Ina da ‘ya’ya mata biyu kafin na aure shi masu shekaru 11 da 18, muna rayuwa dasu amma ban yarda da mijina ba saboda yana da son mata.”

Bai mutunta ni

Ta kara da cewa:

“Mijina ya na sauya mata a duk lokacin da yaga dama kuma ba ya mutunta ni a matsayin mata, idan har kotu ba ta raba auren ba, ni zan gudu da ‘ya’ya na.”

Rahotanni sun tattaro matar na cewa makwabtansu har dariyanta suke saboda sanin halin mijinta na son mata.

Matar ta ce:

“Na gaji da zama dashi, Segun ba zai sauya ba, kullum halinsa kawai bin mata ne.”

Mai karar ta kara da cewa mijin nata ba ya kula da ‘ya’yansu.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Samu Nasarar Kubutar da Saratu, Daya Daga Cikin Yan Matan Chibok A Sambisa

Martanin mijin akan tuhumar da kotun ke yi akansa

Da yake mai da martani, Segun mai shekaru 46 ya amsa duk laifukan da ake tuhumarsa akansu.

A cewar mijin:

“Ba zan yi karya ba, ina kawo mata gidannan amma nayi alkawari zan gyara halaye na, ina rokonta yafiya.”
“Kamar yadda kuke gani matata bul-bul take alaman ba ta shan wahala, kwanan nan na siya mata wayar tafi da gidanka kuma ina biyan kudin makarantar yara.”

Ya roki kotu ta ki raba auren

Segun ya yi alkawarin gyara halayensa yayin da roki kotun ta kara ba shi dama saboda bai shirya rabuwa da matar ba.

Alkalin kotun, Mista Adewale Adegoke ya dage sauraran karar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu don samun daidaito a tsakaninsu.

Fasto Ya Roki Alkali Kada Ya Datse Igiyar Aurensa da Matarsa

A wani labarin, wani Fasto a birnin tarayya Abuja ya roki kotu da kada ta datse aurensa da matarsa saboda yana matukar son ta.

Faston mai suna Lucky Omoha ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tuhumar da ake yi akansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel