Dalilin 'Yan Kasuwa na Dakatar da Sayen Fetur daga Dangote
- Wasu daga cikin dillalan man fetur sun dakatar da sayen fetur daga matatar Dangote saboda rashin tabbas kan sabon tsarin farashi
- Gwamnatin tarayya da matatar Dangote na ci gaba da tattaunawa kan batun sayar da fetur da Dala da kuma samar da danyen mai
- Sai dai hukumar kae hakkin mai saye ta rFCCPC ta ce Naira ce kaɗai halastacciyar kuɗin da ake amfani da ita wajen kasuwancin cikin gida a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Rikici kan sabon tsarin farashin fetur da matatar Dangote ta bullo da shi ya jefa harkar kasuwancin man fetur cikin rashin tabbas.
Wannan sabon mataki da matatar man Dangote ta dauka ya jawo wasu dillalai sun dakatar da sayen kaya saboda fargabar sauyin farashi.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali: Girgizar kasa mai girma ta afku a Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya da matatar Dangote har yanzu ba su cimma matsaya kan batutuwan da suka haddasa matatar ta fara amfani da tsarin farashin Dala ba.
An dakatar da sayen feturin Dangote
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce dillalai na taka-tsantsan saboda ba su san yadda sabon tsarin farashin zai kasance ba.
A cewarsa, fetur da ake sayarwa a yanzu tsohuwar ajiya ce da aka saya tsakanin N1,250 zuwa N1,300 kan kowace lita.
Ya ce ana kuma jiran sabbin kayayyakin da aka shigo da su da kuma sabon danyen mai domin sanin farashin da za a ɗora musu.
Ukadike ya ce:
"Kowa yana shakkar ɗaukar kaya saboda ba a san ko farashin zai sauka ko zai ƙaru ba bayan an saya."
Ba a dakatar da sayen fetur duka ba
Sakataren IPMAN, Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa ba a dakatar da rabon fetur gaba ɗaya ba, amma adadin man da dillalai ke ɗauka ya ragu sosai.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya
A yankin Kudu maso Yamma, shugaban IPMAN na shiyyar, Oyewole Akanni, ya ce wasu gidajen mai sun rufe na ɗan lokaci saboda rashin samun kaya.

Source: Facebook
Ya ce tun bayan dakatar da sayar da fetur daga matatar Dangote kusan kwanaki huɗu da suka gabata, masu rumbunan mai masu zaman kansu sun ƙara farashi.
Akanni ya ce:
"Ba a samu ƙarancin mai ba, amma akwai yiwuwar farashin ya ƙaru idan wannan yanayi ya ci gaba."
Dangote ya raba fetur kyauta
A baya, mun kawo labarin cewa matatar Dangote ta fara kai fetur kyauta zuwa jihohi shida da Abuja ga masu sayen lita 250,000 ko fiye ba tare da karin kudin sufuri ba a wani sabon yunkuri da ta zo da shi.
Kamfanin ya ci gaba da sayar da fetur kan Naira 1,075 kowace lita tare da ba kwastomomi damar biyan bashi na kwanaki 10, matakin da ake ganin zai iya jawo raguwar farashin man fetur a fadin kasa.
A cewar matatar, shirin kai fetur ba tare da karin kudin sufuri ba ya shafi jihohin Legas, Ogun, Rivers, Kaduna, Delta da kuma Abuja domin saukaka wa abokan huldarsa a wadannan wurare.
Asali: Legit.ng