Ina Matukar Son Matata: Fasto Ya Roki Alkali Kada Ya Datse Igiyar Aurensa

Ina Matukar Son Matata: Fasto Ya Roki Alkali Kada Ya Datse Igiyar Aurensa

  • Wani Fasto ya roki alkalin kotu da ke zamanta a Nyanya a cikin birnin tarayya Abuja da kada ya raba aurensa
  • Ana zargin Faston mai suna Lucky Omoha da hada kai da iyayensa wurin cin zarafin matarsa saboda rashin haihuwa
  • Alkalin kotun Doocivir Yawe ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 30 ga watan Mayu na wannan shekara

Abuja - Wani Fasto mai suna Lucky Omoha, ya roki alkalin kotu dake zamanta a Nyanya cikin birnin Abuja da ya taimaka kada ya raba aurensu da matarsa saboda yana matukar son ta.

Wanda ake karan ya bayyana haka ne da yake kare kansa a kotun bayan matarsa ta kai kararsa bisa zargin cin zarafinta da surakanta suke yi mata.

Kotun magistare/Fasto
Matar Faston ta ce dalilan da yasa take so a raba auren shi ne cin zarafin da iyayensa suke yi mata. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Sannan kuma ta tabbatar cewa ta na fiskantar matsi daga surakanen nata saboda Allah bai basu haihuwa ba a tsawon lokacin da suke zaune, cewar jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

Faston ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina matukar son matata, kuma zan ci gaba da sonta duk da ba mu samu haihuwa ba.
“Na fada wa matata cewa kada ta daga hankalinta Allah zai bamu haihuwa wadanda ba za su mutu ba.”

Ya kara da cewa:

“Ita ma matar ta san ina sonta a zuciyata, kuma ba na goyon bayan abinda iyaye na suke mata.”

Matar fasto ta fadi dalilin da yasa take so a raba auren

Matar da ta shigar da karar mai suna Juliet Omoha ta ce duk da mijin nata ba ya hada kai da iyayen nasa suci zarafinta, amma wasu lokutan ba ya mata ta dadi idan aka samu matsala.

A cewar matar:

“Duk lokacin da muka samu rashin fahimta, mijin nawa yana fada min maganganu da suke da alaka da wadanda iyayensa suke fada min, abin yana min zafi, ba na so na ci gaba da zaman auren nan.”

Kara karanta wannan

"Ka yi hauka ne?": Tashin hankali yayin da mawaki ya kaftawa dan sandan Najeriya mari

Rahotanni sun tattaro cewa Mai shari’a Doocivir Yawe ya daga ci gaba da sauraron karar zuwa 30 ga watan Mayu na wannan shekara.

Matar Aure Za Ta Dawo da Sadakin N80k a Gaban Kotu Don a Raba Aurenta

A wani labarin, wata kotu dake zamanta a jihar Kaduna ta umarci matar aure da ta dawo da kudin sadaki N80,000 don a raba aurensu da mijinta.

Matar mai suna Fatima Muhammad ta ce ta amince ta biya kudin saboda ta gaji da zama da mijin nata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel