Sojoji Sun Samu Nasarar Kubutar da Saratu, Daya Daga Cikin Yan Matan Chibok A Sambisa

Sojoji Sun Samu Nasarar Kubutar da Saratu, Daya Daga Cikin Yan Matan Chibok A Sambisa

  • Rundunar sojin hadin guiwa ta ce ta yi nasarar kubutar da daya daga cikin ‘yan matan Chibok da ake tsare da su
  • Yarinyar da aka kwato mai suna Saratu Dauda mai kimanin shekaru 25 a duniya ta bar ‘ya’yan da haifa a can
  • Yayin da gwamnatin jihar ta yi alkawarin daukar nauyin karatunta har zuwa jami’a don inganta rayuwarta

Jihar Borno - Kwamandan rundunar hadin guiwa ta ‘Operation Hadin Kai’ Manjo Janar Ibrahim Ali ya ce an yi nasarar kwato daya daga cikin ‘yan matan Chibok.

Yarinyar da aka kwato din mai suna Saratu Dauda mai kimanin shekaru 25 ta kubuta ne a ranar 6 ga watan Mayu na wannan shekara a maboyar ‘yan ta’addan dake Ukuba a dajin Sambisa dake jihar Borno.

Sojoji sun kwato Saratu a dajin Sambisa
Sojoji Sun Samu Nasarar Kubutar da Saratu, Daya Daga Cikin ’Yan Matan Chibok a Sambisa, Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Da yake mika Saratu ga kwamishinan mata ta jihar, Hajiya Zuwaira Gambo a ranar Litinin 15 ga watan Mayu a Maiduguri, Janaral Ali ya ce kafin kubutarta Saratu ta auri Abu Yusuf wanda shine yake hada wa kungiyar bama-bamai.

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Ya kara da cewa Saratu ta gudu ta bar ‘ya’ya biyar da mijinta a dajin, yayin da rundunar ke kokarin ceto sauran yaran, cewar jaridar Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Ali ya ce an wuce da ita asibitin sojoji na Maimalari don duba lafiyarta kafin mika ta ga gwamnatin jihar.

“Mungode Allah da samun wannan nasara na ceto Saratu, hakan zai taimaka mata ta samu ingattacciyar rayuwa da iyayenta da sauran ‘yan uwa.” in ji shi.

sojojin sun bayyana yadda aka kubutar da sauran 'yan matan Chibok

Bayan haka, ya tabbatar da cewa daga cikin yara 276 da aka sace a shekarar 2014, 76 sun tsira yayin da 107 ‘yan ta’addan da kansu suka sake su a shekarar 2018, cewar Rahotannin da muka samu.

Ya kara da cewa 186 rundunar ce ta kubutar dasu yayin da har yanzu yara mata 93 suke hannun ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

Da ta ke mai da martani, Hajiya Zuwaira ta tabbatar wa ‘yan jaridu cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin karatun Saratu har jami’a.

Kwamishinar ta kara da cewa za a dauki Saratu zuwa gidan gyaran tarbiya da sauya halaye na Bulumkutu a cikin Maiduguri don hada su da sauran wadanda ke samun horo don zama mutanen kirki da kuma dogaro da kansu, inda ta yi addu’an ubangiji ya kubutar da sauran ‘yan matan.

Sojoji Sun Gano Wani Makeken Rami Dauke Da Makamai a Dajin Sambisa

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta gano wani katon rami dauke da muggan makamai a Sambisa.

Makaman wadda suka hada da bama-bamai da muggan makamai an yi nasarar samun su ne bayan samamen da rundunar ta kai a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel