Dawo-Dawo: Dan Takarar Sanatan SDP a Bauchi, Ibrahim Baba Ya Sake Komawa APC

Dawo-Dawo: Dan Takarar Sanatan SDP a Bauchi, Ibrahim Baba Ya Sake Komawa APC

  • Tsohon dan takarar sanatan Bauchi, Hon. Ibrahim Mohammed Baba ya kaura daga jam’iyyar SDP ya sake komawa APC
  • Tsohon mamban majalisar wakilan ya fadi hakan ne a ranar Asabar 13 ga watan Mayu a Azare, Hedkwatar karamar hukumar Katagum
  • Baba ya taba wakiltar mazabar Katagum a majalisar wakilai ta kasa a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 a jam’iyyar APC

Azare, jihar Bauchi - Dan takarar sanatan SDP a zaben 2023, Hon. Ibrahim Mohammed Baba ya bar jam’iyyar, ya sake komawa jam’iyyar APC.

Baba ya tsaya takarar majalisar dattawa ne a mazabar Bauchi ta Arewa a zaben 2023 da aka kammala a watan Faburairu, rahoton Tribune Online.

Hakazalika, ya kasance tsohon dan majalisa mai wakiltar Katagum a majalisar wakilai tsakanin 2015 zuwa 2019 a karkashin inuwar APC.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Baba ya shiga jam’iyyar SDP ne tare da yin takarar sanata a cikinta, inda ya fadi a zaben 2023, sai kuma ya alanta barinta tare da komawa gidansa na baya; APC.

Bayan shan kaye a SDP, dan takarar sanata ya sake komawa APC
Dan takarar sanatan SDP da ya sake komawa APC | Hoto: Ibrahim Adamu Katagum
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin da yasa ya bar SDP

Fitaccen dan siyasar na Arewa ya alanta barin SDP a ranar Asabar 13 ga watan Mayi a garin Azare, hedkwatar karamar hukumar Katagum, kamar yadda Daily Sun ta ruwaito.

Ya samu tarbar jiga-jigan APC, ciki har da shugabanta na gundumar Nasarawa Bakin Kasuwa a Azare, Malam Adamu Abubakar.

A baya, Baba na da matsaloli da yawa da shugabancin APC gabanin zaben 2019, don haka ya barta ya koma SDP tare da yin takarar sanata.

Ya bayyana cewa, ya sake dawowa APC don ba da gudunmawarsa ga ci gaban Najeriya baki daya.

Daga bakin Baba, dalilin dawowarsa APC

Kara karanta wannan

Daga Buhari Zuwa Dogara: Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Wakilai Tun 1999 Zuwa Yanzu

Da yake jawabi, ya ce:

“Babban dalilin dawowa ta APC shine don shiga a warware wasu matsalolin jam’iyyar tare da daura ta kan turba gabanin zaben da ke tafe a gaba.
“Wasu mambobin APC a jihar Bauchi na da dalilai mabambanta na barin jam’iyyar, wasu sun fusata saboda an ware su, musamman a lokacin zabukan fidda gwani.
“Wannan ne yasa wasu daga cikinmu suka yanke shawarin dawowa cikin APC domin farfado da ita.”

Tinubu zai mulki Najeriya da kyau

A wani labarin, hadimin Tinubu ya bayyana cewa, uban gidansa zai mulki Najeriya ne a lokacin da yake zaune a cikinta.

Ya ce shugaban ba zai zama mai yawan gantali zuwa wasu kasashe daba-daban ba kamar yadda ake tsammani.

Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da Tinubu da Buhari suka tafi kasar waje saboda wasu dalilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel