Daga Buhari Zuwa Dogara: Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Wakilai Tun 1999 Zuwa Yanzu

Daga Buhari Zuwa Dogara: Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Wakilai Tun 1999 Zuwa Yanzu

  • Tun bayan dawowar dimukradiyar Najeriya a 1999, majalisar ta samu shugabanni akalla guda takwas, maza 7 da mace guda 1
  • Shiyyar Arewa maso Yamma ita ta mamaye shugabancin kujerar majalisar, saboda hudu daga cikin takwas daga shiyyar suke
  • A majalisar kuma an samu mace ta farko da ta zama shugabar majalisar, sannan akwai wanda yafi kowa karancin shekaru

Tun bayan da jam’iyya mai mulki ta APC ta tura shugabancin majalisar wakilai ta 10 Arewa maso Yamma, ake ta samun hatsaniya da cece-kuce ta ko ina a fadin kasar.

Jam’iyyar APC ta sanar da cewa ta zabi Abbas Tajudden dan majalisa daga jihar Kaduna a matsayin wanda zai gaji kujarar Femi Gbajabiamila.

majalisa
Shugabannin majalisar wakilai, Hoto: Femi, Dogara, Bankole, Etteh, Masari
Asali: Facebook

Zaban nashi ya jawo korafe-korafe daga sauran takwarorinsa ‘yan majalisa da gwamnoni da sauran kungiyoyi.

Abin tambaya anan shi ne, “shin jam’iyyar APC mai mulki za ta shanye matsin lamba daga wurin wadannan ‘yan siyasa da kuma majalisar kanta?”

Kara karanta wannan

Hotuna: Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 6 Masu Neman Shugabanci Sun Gana da Shugabannin APC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun lokacin da dimukradiya ta dawo kasar a shekarar 1999, Shugabannin 8 ne suka jagoranci majalisar.

Jaridar Legit ta tattaro jerin sunayen shugabannin majalisar ce, yankinsu da kuma jihohinsu:

1. Salisu Buhari (1999-2000) – Arewa maso Yamma/Jihar Kano

Salisu Buhari shi ne farkon wanda ya fara shugabantar majalisar a jamhuriya ta hudu. Salisu bai dade akan shugabancin majalisar ba saboda makwanni 6 kadai ya yi akan kujerar majalisar bayan an bankado wasu bayanai da suka nuna cewa ya yi karya dangane da shekarunsa da kuma takardun karatunsa.

Ya bayyana cewa an haife shi a shekarar 1970, sabanin 1963.

Bayan kammala bincike, an yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kaso.

2. Ghali Na'Abba (2000-2003) - Arewa maso Yamma/Jihar Kano

An haife shi a ranar 27 ga watan Satumba ta shekarar 1958, Ghali Na’Abba ya gaji kujerar Salisu tun daga shekarar 2000 zuwa 2003.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 5 Na APC Da Suka Lashi Takobin Yaƙar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

Ya kammala karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya karanci Kimiyyar Siyasa a shekarar 1979.

3. Aminu Bello Masari (2003-2007) - Arewa maso Yamma/Jihar Katsina

Aminu Bello Masari shima ya fito daga Arewa maso Yamma, daga jihar Katsina, ya jagoranci majalisar tun daga shekarar 2003 zuwa 2007,.

A yanzu haka shi ne gwamnan jihar Katsina wadda ita ce kuma jihar da shugaban kasa Buhari ya fito.

4. Patricia Etteh (2007) - Kudu maso Yamma/Jihar Osun

A karshe dai, jagorancin ya bar Arewa maso Yamma ya koma Kudu maso Yamma amma ba ta dade sosai ba.

Patricia Etteh ita ce mace ta farko da ta jagoranci majalisar wakilan Najeriya, ta yi jagoranci na dan kankanin lokaci wadda a cikin shekarar 2007 din ta hau kujerar aka tsige ta.

Patricia ‘yar asalin jihar Osun ce.

5. Dimeji Bankole (2007-2011) - Kudu maso Yamma/Jihar Ogun

Kujerar majalisar ba ta bar Kudu maso Yamma ba inda Dimeji Bankole ya karbi jagorancin majalisar wanda shi kuma ya kasance dan asalin jihar Ogun daga Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Betara Ya Yi Fatali Da APC, Ya Nuna Sha’awarsa Ta Tsayawa Takara

Bankole shi ne ya kafa tarihi na zama shugaban majalisa mafi karancin shekaru 37, ya yi jagoranci daga shekarar 2007 zuwa 2011.

6. Aminu Waziri Tambuwal (2011-2015) - Arewa maso Yamma/Jihar Sokoto

Arewa maso Yamma ta ci gaba da mamayar kujerar majalisar inda Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci majalisar daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Tambuwal wanda dan asalin jihar Sokoto ne kuma yanzu haka shine gwamnan jihar mai barin gado bayan Hukumar Zabe mai zaman kanta ta sanar da shi a matsayin sanata a zaben gama-gari da aka gudanar a farkon shekaran nan.

7. Yakubu Dogara (2015-2019) - Arewa maso Gabas/Jihar Bauchi

Yakubu Dogara dan majalisa mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa dake jihar Bauchi ya jagoranci shugabancin majalisar tun daga shekarar 2015 zuwa 2019.

8. Femi Gbajabiamila (2019 - zuwa yanzu) - Kudu maso Yamma/Jihar Lagos

Femi Gbajabiamila shi ne shugaban majalisar a yanzu wanda ya fito daga jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Arewa maso Yamma ta samu Shugabancin majalisar wakilai da dattawa a APC

Femi ya karbi jagorancin majalisar ne tun daga shkarar 2019 har zuwa yau, kafin zama shugaban majalisar, Gbajabiamila shi ne mamban majalisar na farko da aka zaba a shekarar 2003.

Rahotanni sun tabbatar cewa na daya daga cikin manya-manyan yaran zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu.

Gwamna Adeleke da Wasu Gwamnoni 4 da Suka Yi Nasara a Kotu

A Najeriya, duk bayan zabubbuka ana korafe-korafe daga wasu da abin bai musu dadi ba, saboda haka ake zuwa kotu inda ake shafe watanni ko shekaru ana shari’a.

Ga jerin sunayen gwamnoni 5 da suka yi nasarar kwace mulki a hannun takwarorinsu ta hanyar kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel