Yawaita Zuwa Turai: Hadimin Tinubu Ya Ce Mai Gidansa Zai Yi Mulkinsa a Najeriya, Ba Zai Tare a Turai Ba

Yawaita Zuwa Turai: Hadimin Tinubu Ya Ce Mai Gidansa Zai Yi Mulkinsa a Najeriya, Ba Zai Tare a Turai Ba

  • Zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu zai yi aikinsa a duk inda yake, inji hadiminsa a wata tattaunawa
  • Ana ta yada cece-kuce da jita-jitar Tinubu zai iya zama kamar Buhari, zai ke yawan barin kasar zuwa wasu kasashe
  • A halin da ake ciki, shugaba Buhari da zababben shugaban kasa Tinubu suna can a Landan, jama’a na ta magana

FCT, Abuja - Bayo Onanuga, mai magana da yawun zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya ce mai gidansa ba zai yi mulkin kasar nan daga kasashen waje ba kamar yadda wasu ke fadi.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa a shirin Daily Politics na Trust Tv, inda ya bayyana abubuwan da Tinubu zai yi a kwanakinsa 10 na farko a ofishin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ba Zai Manta Ganduje, El-Rufai, Sauran Gwamnonin Arewa a Rabon Mukamai ba

Ya yi martani ga batun da wasu ke cewa Tinubu zai mulki Najeriya ne daga Landan kamar yadda Buhari ya yi a wasu lokuta.

Tinubu zai zauna ya mulki Najeriya, ya yawo, inji hadiminsa
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A cewar Onanuga, hakan ba zai faru da zababben shugaban kasar na Najeriya ba, ya kuma bayyana dalilinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An dami Tinubu da neman kujeru a mulkinsa

A cewarsa:

“Ba za ku fahimci irin matsin lambar da mutanen da ke neman kujeru a gwamnatin nan ke yi ba ta hanyar kwamitoci, baya ga batun zababben shugaban kasa. Mutane na ta turo duk wasu nau’ikan bukatu.
“Don haka, kamar yadda sanarwa ta bayyana, tafiyarsa ba komai bace sai don kuje wa matsin lamba da damuwa.
“Ya tafi Landan ne don duba jikokinsa, amma daga baya ma ya yanke shawarin ba zai je ba. Ya dawo gida a madadin hakan.

Kara karanta wannan

Hasashen ci gaba: Ana yiwa Najeriya kyakkyawar fata, amma kash, Obasanjo ya magantu

“Hakazalika, ya kasance a Saudiyya kafin zabe, don haka ya yanke shawarin ba zai koma ba. Don haka ya yanke shawarin fasa wadannan sannan ya dawo gida.”

Tinubu zai yi mulkinsa daram, ba a kasar waje ba

Game da batun zaman Tinubu a Najeriya da kuma fuskantar dukkan matsalolin kasar, hadimin nasa ya ce:

“Na yi imanin zai yi hakan. Amma yanzu ka san muna rayuwa ne a duniya dunkulliya, kamar yadda suke fadi.
“Don haka, ko da yana kasar Rasha ne, zai iya bayyana ta Zoom sannan zai iya yin komai. Amma zan tabbatar maka cewa zai zauna dirsham ya yi aikinsa. Ba zai zama shugaban da bai zama ba.”

A halin da ake ciki, an yi arashin kasancewar shugaban kasa Buhari da zababben shugaba Tinubu suna can a Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel