Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani, ya rasa matar sa wacce ta riga mu gidan gaskiya
  • Mrs Jane Nnamani ta koma ga mahaliccin ta a ranar Alhamis ta satin da ya gabata a birnin Enugu
  • Marigayiyar ta mutu ne a asibiti inda ta je domin a yi mata wata ƴar gajeruwar tiyata

Jihar Enugu - Misis Jane Nnamani, matar tsohon shugaban majalisar dattawa, Cif Ken Nnamani, ta koma ga mahaliccinta, rahoton Punch ya tabbatar.

Mrs Nnamani, wacce shekarunta a duniya sun kai 60, ta rasu ne a asibitin National Orthopedic, da ke birnin Enugu, a ranar Alhamis da ta gabata, 4 ga watan Mayu 2023, inda ta je yi mata ƴar gajeruwar tiyata.

Matar Ken Nnamani ta mutu
Mrs Jane Nnamani ta mutu tana da kusan shekara 60 Hoto: Ken Nnamani
Asali: Twitter

SaharaReporters ta kawo rahoto cewa mutuwarta ta kawo ruɗani a cikin iyalanta, domin har yanzi ba a sanar da mijinta wanda yana ƙasar waje neman lafiya, labarin mutuwarta ba.

Kara karanta wannan

Ke Duniya: Wata Budurwa Ta Maka Mahaifinta a Gaban Kotun Shari'ar Musulunci Kan Dalili 1 Rak

A cewar wata majiya:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

a, ƴaƴanta da su ke a ƙasar waje, ba su da labarin cewa mahaifiyar su ta je asibitin domin a yi mata tiyata.

Ƴar autar ta wacce ta ke a Enugu, ita ma bata san cewa mahaifiyarta bata da lafiya ba, har sai da labarin mutuwarta ya riske ta.

Mrs Nnamani ta dai je asibitin ne domin a yi mata tiyata tare da ƴar aikinta da direban ta, ba tare da ta sanar da ɗiyar ta ba.

Wata majiyar ta ƙara da cewa:

"Duk da cewa ta mutu, babu wanda a cikin ahalinta ya isa ya sanar da labarin mutuwarta, har sai mijinta ya ga gawarta."
"Kuma duk cikin ƴaƴanta maza, babu wanda ya ke a ƙasar nan, sannan ƴar autar ta wacce ta ke a Enugu, ba ta san yadda za ta yi ba kan sanar da mutuwarta."

Kara karanta wannan

"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari

Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, tsohon shugaban majalisar dattawan, bai fitar da sanarwa ba kan mutuwar matarsa.

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC, Baba Lankondaro, Ya Mutu

A wani rahoton na daban kuma, tohon shugaban ƙungiyar kwallon kafa 'Shooting Stars Sports Club (3SC), Pa Olayiwola Olakojo, ya mutu koma ga mahaliccin sa.

Olayiwola wanda ake yi wa kallon masoyin ƙwallon ƙafa da yafi kowa daɗewa a Najeriya, ya bar duniya yana da shekara 111

Asali: Legit.ng

Online view pixel