Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC, Baba Lankondaro, Ya Mutu

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC, Baba Lankondaro, Ya Mutu

  • Tsohon shugaban kungiyar 3SC kuma masoyin kwallon kafa mafi tsufa a Najeriya, Baba Lankondoro, ya kwanta dama
  • Mista Olaniyan, shugabam 3SC ya tabbatar da rasur jigon ƙungiyar da safiyar Alhamis, yace zasu je ta'aziyya har gida
  • Marigayi Baba Lankondoro ya rasu ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu, 2023 yana da shekaru 111 a duniya

Oyo- Tsohon shugaban ƙungiyar kwallon kafa 'Shooting Stars Sports Club (3SC)' kuma wanda ake hasahen shi ne masoyin wasan kwallo mafi tsufa a Najeriya, Pa Olayiwola Olakojo, ya mutu.

Leadership ta rahoto cewa mamacin wanda yafi shahara da sunan Baba Lankondoro, ya kwanta dama yana da shekaru 111 a duniya, kamar yadda aka sanar yau Alhamis.

Pa Olayiwola Olakojo.
Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC, Baba Lankondaro, Ya Mutu Hoto: leadership
Asali: UGC

Shugaban 3SC na yanzu, Babatunde Olaniyan, ne ya tabbatar da mutuwar tsohon jigon ƙungiyar a wata hira ta wayar salula, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Adadin 'Yan Najeriya Da Ta Tsamo Daga Kangin Talauci a 2022

Olaniyan ya ce ƙungiyar ta samu labarin mutuwar Pa Lakondoro ranar Alhamis kuma suna shirye-shiryen kai ziyarar ta'aziyya ga iyalansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina tabbatar muku da cewa ya rasu da safiyar nan kuma tuni muka fara shirin zuwa gidansa ta'aziyya," inji shi.

An haife shi a ranar 7 ga watan Janairu, 1912 a cikin 'yan addinin gargajiya da ke zaune a kauyen Ile Otun, yankin Oje a ƙaramar hukumar Ibadan ta arewa, jihar Oyo.

Haka zalika bayanai sun nuna cewa asalinsa ɗan kauyen Saago Idiiya ne wanda ke karkashin ƙaramar hukumar Ido, duk a jihar Oyo, kudu maso yammacin Najeriya.

Marigayi Pa Lankondoro ya yi karatu a makarantar Oke Are Theological Seminary, da ke Ibadan da kuma makarantar St Finnbar, jihar Legas.

Daga bisani ya shiga rundunar sojin 'yan mulkin mallaka ta yaƙin duniya na biyu kuma hakan ya sa ya ziyarci ƙasashen Scotland, India, Trimia da sauransu tare da marigayi Olubadan na ƙasar Ibadan, Oba Samuel Odulana Odugade.

Kara karanta wannan

Zargin Ta'addanci: Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokoki a Arewa Ya Yi Murabus, An Naɗa Sabo

Jami'in Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu a Hannun Yan Bindiga

A wani labarin kuma kun ji cewa Wani Babban Jami'in Kotun Musulunci Ya Rasu Ta Hanya Mai Ban Tausayi a Watan Azumi

Wani mazaunin Ibbi, garin da Kotun da marigayin ke aiki take a karamar hukumar Mashegu, jihar Neja, ya ce lamarin ba shi kaɗai ya shafa.

A cewarsa, bayan ma'aikacin Kotun akwai wasu bayin Allah da yan bindigan suka kashe bayan sun yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel