Kamfanin Dangote Da Sauran Jerin Kamfanonin Da Suka Tafka Asara a Farkon 2023

Kamfanin Dangote Da Sauran Jerin Kamfanonin Da Suka Tafka Asara a Farkon 2023

  • Kamfanoni 6 na Najeriya sun fuskanci koma baya a kuɗaɗen shigar da suka samu a watanni 3 na farkon shekarar 2023.
  • Kamfanonin sun alaƙanta wannan ƙasan da kuɗaɗen shigar su suka yi akan ƙalubale da dama, ciki har da sauya fasalin naira
  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da janye tsaffin takardun kuɗin N1000, N500, da N200 a watan Fabrairu, wanda hakan ya haifar da ƙarancin kuɗi

Kamfanunnikan Najeriya a ɓangarori daban-daban, sun fuskanci ƙalubale da dama a watan ukun farkon shekarar 2023, saboda ƙarancin cinikin da aka samu wanda ƙarancin kuɗi ya haifar.

A kammalallen rahoton da aka miƙa a kasuwar hada-hada ta Najeriya, kamfanoni shida sun samu ragowar samun kuɗin shiga wanda ya kai N46.52bn, a wata uku na farkon shekarar 2023.

Kamfanonin Najeriya 6 sun yi asara a farkon 2023
Kamfanin sun ji a jika a farkon shekarar 2023 Hoto: NGX
Asali: Facebook

Kamfanonin da abin ya shafa sun haɗa da Dangote Cement Plc, UAC of Nigeria Plc (UACN), Nigerian Breweries Plc, da Notore Chemical Industries Plc.

Sauran sun haɗa da GlaxoSmithKline Consumer Nigeria Plc da ABC Transport Plc.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗannan kamfanonin sun samu kuɗin shiga da suka kai N559.14bn a wata ukun farko na shekarar 2023, saɓanin N605.66bn da suka samu a daidai irin wannan lokacin a shekarar 2022.

Misali, kamfanin Dangote Cement Plc, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin siminti a Afrika, kuɗin shigar sa ya ragu da kaso 1.62%, haka kamfanin Nigerian Breweries Plc, kuɗin shigar sa ya ragu da 10.47%.

Haka shi ma kamfanin UAC of Nigeria Plc (UACN), babban kamfani wanda ya ke harkokin abinci da kayan sha, gine-gine, da fenti ya samu ragowar kuɗin shiga da kaso 11.20%.

Kamfanin taki na Notore Chemical Industries Plc, samun kuɗin shigar sa ya ragu da kaso 75.26%.

Haka kuma, kamfanin GlaxoSmithKline Consumer Nigeria Plc, kuɗin shigar sa yayo ƙasa warwas da kaso 45.37% .

Yayin da kamfanin sufuri na ABC Transport Plc, ya samu ragowar kaso 22.46% na kuɗin shigar sa.

Jerin kuɗaɗen shigar kamfanonin a wata ukun farko na 2023 da 2022

  • Dangote Cement Plc: Kuɗin shigar 2023 - N406.7bn, kuɗin shigar 2022 - N413.4bn.
  • UAC of Nigeria Plc: Kuɗin shigar 2023 - N24.6bn, kuɗin shigar 2022 - N27.7bn.
  • Nigerian Breweries Plc: Kuɗin shigar 2023 - N123.31bn, kuɗin shigar 2022 - N137.77bn.
  • Notore Chemical Industries Plc: Kuɗin shigar 2023 - N4.10 billion, kuɗin shigar 2022 - N16.56bn.
  • GlaxoSmithKline Consumer Nigeria Plc: Kuɗin shigar 2023 - N4.02bn, kuɗin shigar 2022bn - N7.36bn.
  • ABC Transport Plc: Kuɗin shigar 2023 - N1.45bn, kuɗin shigar 2022 - N1.87bn.

Baya Ga Dangote, an Fara Samun Sabbin Attajirai da Ke Tasowa a Nahiyar Afrika

A wani rahoton kuma, kun ji cewa akwai sabbin attajirai da ke tasowa a nahiyar Afrika, bayan Aliko Dangote.

Dangote ya kasance attajirin da babu kamar sa kaf a nahiyar Afrika, sai dai yanzu an fara samun sabbin attajirai a nahiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel