Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Hukumar Yan Sanda a Jihar Anambra

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Hukumar Yan Sanda a Jihar Anambra

  • 'Yan bindiga sun farmaki shingen bincike, sun kashe 'yan sanda uku ranar Alhamis a jihar Anambra
  • Wani mazauni ya ce tun da lamarin ya faru, baki ɗaya mutanen yankin suka kulle wuraren sana'arsu suka yi takansu
  • Mai magana da yawun 'yan sanda ya ce wannan ɗaya ne daga cikin harajin da jami'an tsaro ke biya a bakin aiki

Anambra - Tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda uku a garin Umunze, ƙaramar hukumar Orumba ta kudu a jihar Anambra.

The Cable ta rahoto cewa 'yan sandan sun gamu da ajalinsu ne ranar Alhamis, yayin da 'yan bindigan suka kai farmaki shingen bincike da ke kan titin Umunze-Ihite.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Hukumar Yan Sanda a Jihar Anambra Hoto: thecable
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindiga sun dira shingen binciken ba zato ba tsammani, suka buɗe wa yan sandan da ke bakin aiki wuta, nan take suka kashe uku.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗi Matsalar da Aka Samu Da halin da Ragowar 'Yan Najeriya Ke Ciki a Sudan

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yankin ya zama tamkar kufai, masu shaguna sun rufe wurin sana'arsu saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Lamarin ya faru da safe, yan bindiga suka kashe yan sanda uku, kowane farar hula ya yi takansa saboda harsasai ne kawai suke cin kasuwa a nan," inji shi.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Anambra, Tochuckwu Ikenga, ya tabbatar da kisan jami'an guda uku ranar Alhamis.

A ruwayar The Nation, Ikenga ya ce hare-haren yan bindiga da sauran yan ta'adda na ɗaya daga cikin abubuwan da dakarun yan sanda ke fuskanta yayin da suke kan aiki.

Ya ƙara da cewa irin waɗan nan hare-hare ba zasu sa jami'an yan sanda su ja da baya ba, inda ya ce tuni hukumar ta kaddamar da aikin farautan makasan domin kamo su.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Jami'in Ɗan Sanda Ta Wani Yanayi Mai Ban Tausayi

A kalamansa, kakakin yan sandan ya ce:

"Tuni muka tura karin dakaru zuwa yankin kuma a yanzun sun baza koma ta ko ina suna farautar makasan. Haka nan mun fara sintirin haɗin guiwa ba kama hannun yaro a yankin."

Sojoji sun samu nasara a Borno

A wani labarin kuma Dakarun Soji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai da Yan Ta'adda Suka Sace a jihar Borno

Jami'an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar kwato ma'aikatan NGO biyu cikin uku da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar Borno, arewa maso gabas.

Tun da labarin garkuwa da ma'aikatan ya bayyana, mahukunta ba su ce komai har kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel