Nasara Daga Allah: Sojoji Sun Sheke Shugaban 'Yan Bindiga, Da Kwamushe Masu Ba Su Bayanan Sirri

Nasara Daga Allah: Sojoji Sun Sheke Shugaban 'Yan Bindiga, Da Kwamushe Masu Ba Su Bayanan Sirri

  • Sojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga fiye da goma tare da kwamushe shugabansu da ke Danko-Wasagu a jihar Kebbi
  • Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana nasarar bisa jajircewan jami’ansu in da ya ce an kuma kama mutane da ke da alaka da harin
  • Ya bayyana irin muggan makaman da aka samu a wurin ‘yan bindiga da suka hada da awaki da shanu da mashuna da sauransu

Jihar Kebbi - Rundunar sojin Najeriya ta hallaka akalla ‘yan bindiga 14 a wani farmaki da ta kai tare da kwamushe shugaban ‘yan ta’addan a Arewa maso yammacin Najeriya.

Sojin hadin gwiwar sama da kuma kasa ne su ka kai wannan farmaki a cikin dajin wani kauye da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Babu Shiri: Gwamnati Ta Yi Bayani Kan Matsayarta Game Da Cusa Tubabbun ’Yan Boko Haram Cikin Al’umma

sojoji
Sojojin Najeriya, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Manjo janar Musa Danmadami shi ne ya bayyan haka ga ‘yan jaridu a Abuja, in da ya tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun jikkata sakamakon harin, Daily Trust ta tattaro.

Karin bayani daga bakin Manjo Janar Musa

A wani rahoton, Manjo Janar Musa ya kara da cewa sojoji sun kuma kama akalla mutane 6 da ake zargin suna bai wa ‘yan ta’addan bayanan sirri da yake jawo asarar rayuka sakamakon hare-haren ‘yan ta’addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Tsakanin 21 zuwa 25 ga watan Afrilu, jami’anmu sun kai sumame kananan hukumomin Danko- Wasagu a jihar Kebbi da kuma Bungudu da Zurmi da Maradun a jihar Zamfara, sannan kananan hukumomin Faskari a jihar Katsina da kuma Tangaza na jihar Sokoto.
“Bayan kai ruwa rana da aka yi, sojoji sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda 14 ciki har da shugabansu tare da kama mutane 30 wadanda suke basu bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗi Matsalar da Aka Samu Da halin da Ragowar 'Yan Najeriya Ke Ciki a Sudan

Makaman da aka samu

Ya bayyana irin muggan makaman da suka kwato a wurin ‘yan bindigan da suka hada da AK-47 guda 5, mashuna 20 da shanu 24 da adduna guda 3, da kuma awaki guda 102 da tsabar kudi N6,900 da sauran muggan makamai.

Sojojin Najeriya Sun Cafke Wani Basarake Mai Hada Baki Da 'Yan Bindiga a Kaduna

A wani labarin, Sojoji sun kai sumame a ƙauyen Janjala cikin ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, inda suka cafke Madakin Janjala, Mallam Ibrahim Aliyu, da wasu mutum 13 masu ba ƴan bindiga bayanai.

Wani majiya wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya gayawa jaridar Daily Trust cewa, sojojin sun shigo garin ne ranar Talata akan motoci 8 ƙirar Hilux, da babura sannan suka tafi da waɗanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel