Babu Shiri: Gwamnati Ta Yi Bayani Kan Matsayarta Game da Cusa Tubabbun ’Yan Boko Haram Cikin Al’umma

Babu Shiri: Gwamnati Ta Yi Bayani Kan Matsayarta Game da Cusa Tubabbun ’Yan Boko Haram Cikin Al’umma

  • Kwamishinan Gyara da Farfado da Gine-gine na jihar Borno, yace gwamnatin jihar na kokarin ganin an dawo da tababbun ‘yan Boko Haram gidajensu
  • Mutane da dama suna nuna fargaban dawo da ‘yan Boko Haram din gida musamman kada su sake far musu bayan sun dawo
  • Gwamnatin jihar da Majlisar Dinkin Duniya na kokarin samar da yanayi mai kyau don dawo da su cikin iyalansu

Jihar Borno - Kwamishinan Gyara da Farfado da Gine-gine na jihar Borno, Mustapha Gubio ya ce zai yi wahala su dawo da tubabbun ‘yan Boko Haram cikin al’ummarsu nan kusa.

Mustapha Gubio ya ce gwamnatin jihar Borno da Majalisar Dinkin Duniya suna kokarin samar da wani yanayi da zai sake sa a dawo da ‘yan Boko Haram din cikin al’ummarsu.

Gwamnatin jihar Borno tace babu wani shiri nan kusa don dawo da tubabbun 'yan Boko Haram gidajensu
Tubabbun 'yan Boko Haram : Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Kimanin shekaru biyu kenan tun bayan da ‘yan ta’addan suka mika makamansu, gwamnatin jihar ta dauki alwashin dawo da tubabbun ‘yan Boko Haram din gidajensu, amma kuma mutane da dama suna nuna fargaban cewa komai na iya faruwa in har aka dawo da su cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya Ya Zama Sabon Shugaba

Garuruwa da dama sun sha fama hare-haren ‘yan ta’addan musamman Bama lokacin da suka kai farmaki da yi wa mutane fiye da 200 yanakan rago, sun ce baza su taba yafe wa ‘yan ta’addan ba, jaridar Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin tubabbun ‘yan Boko Haram

Ba a san iya adadin tubabbun ‘yan Boko Haram din ba, a cewar gwamnatin jihar da rundunar tsaro ganin cewa har yanzu suna cigaba da karban wasu tubabbun.

Tubabbun ‘yan ta’addan da iyalansu yanzu haka suna killace a wuri mai tsaro tare da samun kulawa ma musamman daga gwamnatin jihar.

Gubio ya ce:

“Sauran tubabbun musamman mata da yara, an dawo da su cikin al’umma don daidaituwar halayensu bayan tattaunawa da wadanda abun shafa.
“Sannan tubabbun ‘yan Boko Haram din ba za a sake su ba har sai gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya ta samar da wurin zama na musamman don gudun daukar fansa daga al’umma.

Kara karanta wannan

Allah Ya yi, Saitin Farkon ‘Yan Najeriya 350 da Yaki Ya Rutsa da su a Sudan Sun Dawo

Gubio ya yi wannan bayani ne ga manema labarai bayan gabatar da wani lakca a Hukumar Koyar da Tsaro a Maiduguri ranar Alhamis 4 ga watan Mayu.

Garuruwan da Boko Haram suka daidaita

Kwamishinan tabbatar da cewa 12 daga cikin daruruwan al’ummomin da Boko Haram suka daidaita sun dawo cigaba da rayuwa tun shekarar 2019.

“Yace za a sake dawo da akalla al’ummomi 6 muhallansu”

Dakarun Sojin Najeriya sun ceto ma'aikatan NGO 2 daga hannun yan ta'adda a Borno

A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar ceto karin ma’aikatan jin kai wadanda ke aiki da Family Health International (FHI360) a jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mazauna yankin sun tabbatar da samun wannan nasara a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel