Yan Sanda a Jihar Kogi Sunyi Nasarar Kwamushe Kasurgumin Mai Garkuwa Da Ya Addabi Jama'a

Yan Sanda a Jihar Kogi Sunyi Nasarar Kwamushe Kasurgumin Mai Garkuwa Da Ya Addabi Jama'a

  • Rundunar yan sandan jihar Ekiti sun tabbatar da nasarar kame wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankuna daban daban na jihar
  • Kwamishinan `yan sandan jihar ne ya tabbatar da hakan bayan ya kai ziyara wa kakakin majalisar jihar don neman goyon bayanta a samar da zaman lafiya
  • Kakakin majalisar a nata jawabin, tayi alkawarin cigaba da bawa jami`an tsaro goyon baya don samar da zaman lafiya mai dorewa.

Jihar Ekiti - Rundunar `yàn sandan jihar Ekiti tace jami`anta sunyi nasarar kama kungurmin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankunan jihar.

Kwamishinan `yan sanda na jihar, Dare Ogundare ne ya bada wannan sanarwar a ranar Laraba 3 ga watan Mayu lokacin da ya kai ziyara wa kakakin majalisar jihar.

yan sanda
Yan Sanda a jihar Kogi Sunyi Nasarar Kwamushe Kasurgumin da ya Addabi Jama`a, Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ogundare ya ce mai garkuwa da mutanen, wanda akafi sani da ‘Danger’ an kama shine a jihar Kogi bayan hukumar ta samu bayanan sirrin inda yake, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara Kan Kujerar Kakakin Majalisa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

‘Tun bayan lokacin dana karbi wannan mukami, nayi nasarar cafke masu laifuffuka daban daban da suka wannan yankunanmu kuma an hukunta mafi yawa daga cikinsu’
“A yau dinnan ma munje har jihar Kogi don kama wannan gagararren mai garkuwa da mutane, Danger, kuma tsare a yanzu haka”.
”Mun tabbatar da cewa duka mashiga da mafitar wannan jiha mun sa jami`an tsaro da kuma karin jami`anmu a ko ina don samar da tsaro”.

Rahotanni sun ce Kwamishinan yana kira ga mazauna wannan yanki da su rinka taimakawa jami`ansu da bayanai da za su taimaka wurin kwamushe 'yan ta`adda a jihar.

Mene kakakin majalisar ta ce

A nata jawabain, kakakin majalisar jihar, Miss Adeluga ta tabbatr da cewa majalisarsu zata ci gaba da bawa jami`an `yan sanda hadin kai don ganin an kare rayuka da dukiyoyin al`umma.

Kara karanta wannan

Assha: Shugaban APC ya ce gwamnan Arewa bai iya komai ba, 'yan sanda sun kwamushe shi

“Jiharmu tana daya daga cikin jihohi masu zaman lafiya, duk da matsalar masu garkuwa da mutane amma dai hakan da dan sauki”.
“Duk inda akwai zaman lafiya to dole za`a samu cigaba da walwala saboda zamuyi kokarin hadaka da jami`an tsaro dan zaman lafiya”

An kama wasu masu tada zaune tsaye

Wannan na zuwane bayan jami`an `yan sanda sunyi nasarar kama wadanda suka haddasa rikicin `yan kungiyar asiri a jihar makwanni biyu da suka wuce.

Gwamna Obaseki na jihar Edo ya sallami kwamishinoni da hadimansa

A wani labarin, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya rushe majalisar zartarwar jihar gabaɗayan ta.

Gwamnan ya ɗauki matakin rushe majalisar zartarwar ne a ranar Laraba, 3 ga watan Mayun 2023, rahoton Tribune ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel