Majalisa Ta 10: Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara Kan Kujerar Kakakin Majalisa

Majalisa Ta 10: Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara Kan Kujerar Kakakin Majalisa

  • An bayyana Ahmed Wase a matsayin wanda ya fi kowa cancanta ya zama kakakin majalisa ta 10
  • Lauya mai rajin kare hakkin bil'adama Frank Tietie ne ya bayar da bayanan akan mataimakin kakakin majalisar
  • Kamar yadda ya bayyana, domin samun adalci da daidaito, dole ne kakakin majalisar ta 10 ya fito daga yankin Arewa ta tsakiya

Babban lauya ɗan rajin kare haƙƙin bil'adama kuma mai sharhi akan al'amuran siyasa Frank Tietie, ya ba wa jam'iyyar APC mai mulki shawara kan cewa mataimakin kakakin majalisar dokoki na yanzu wato Ahmed Wase ne ya fi dacewa da zama shugaban majalisar ta Zango na 10.

Ya bayyana hakan ne a hirar shi da gidan talabijin na Arise Tv ranar Talata, inda ya bayyana cewar akwai buƙatar ace wanda ya fi cancanta ne ya samu shugabancin majalisar zango na 10 kamar yadda legit ng ta wallafa.

Kara karanta wannan

Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar

Ahmed Wase
Frank Tietie ya ce Wase ne ya fi dacewa ya zama shugaban majalisa ta 10: Twitter/ @HonAhmedWase
Asali: Twitter

'Yan majalisu 7 ne ke harin kujerar kakakin majalisar dokoki ta wannan zango

Ya zuwa yanzu dai aƙalla 'yan majalisu bakwai ne waɗanda suka yi nasara a yankunan su a zaɓen da ya gabata suke fafutukar neman wannan kujera ta kakakin majalisar dokoki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mambobin dake neman wannan kujera sun haɗa da shi mataimakin kakakin na yanzu wato Ahmed Wase, Aliyu Betara, Yusuf Gagdi, Tunji Olawu, Taju Abbas, Princess Onuoha, da kuma Benjamin Kalu.

Sai dai lauyan mai rajin kare haƙƙin ɗan adam ya nuna goyon bayan shi ga Wase, inda ya bayyana cewa mutum ne da yake da tarihin gogewa a hidimar mulki kuma mutum ne mai nagarta.

Ahmed Wase ne ya fi kowa cancanta da wannan kujera

Yace indai har cancanta APC za ta bi, to lallai Wase yafi kowa cancanta duba da cewa wannan ne zuwan shi na biyar majalisa. Hakanan kuma ya riƙe kwamitoci da dama a zaman shi na majalisar.

Kara karanta wannan

Rigima Ta Ɓalle, Yan Sanda Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar da PDP Ke Mulki

“Ahmed Wase mutum ne da aka shaide shi da yin biyayya ga jam'iyya sannan kuma mai goyon bayan sabon shugaban ƙasa ne. Haka nan kuma Wase ya taka muhimmiyar Rawa wajen ganin Gbajabiamila ya samar da daidaito a cikin majalisa.” inji lauyan.

Lauyan ya ƙara da cewar akwai bukatar jam'iyyar ta APC tayi la'akari da yanki wajen zaɓar shuwagaban, wanda idan aka yi la'akari da inda ya fito wato Arewa ta Tsakiya za a ga cewa shi ya dace a baiwa kujerar.

A ƙarshen makon nan da ya gabata ne dai jaridar Leadership ta wallafa labarin cewa wasu gungun tsofaffin 'yan majalisar dattawa da na wakilai na jihar Plateau sun nuna goyon bayan su ga Ahmed Wase dangane da kujerar da yake nema.

Mai tsaron lafiyar minista ya bindige shi har lahira

A wani labarin kuma, wani mai tsaron lafiyar wani minista ya bindige ministan da ya ke ba wa tsaro har lahira inda daga bisani shima kuma ya halaka kan sa bayan guduwa da yayi a farko.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne jiya Talata a ƙasar Uganda inda wani daga cikin masu ba wa ƙaramin ministan ƙwadago da masana'antu na ƙasar Kanar Charles Okello Engola ya sa bindiga ya harbe shi har lahira a yayin da yake shirin zuwa wajen aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel