Gaskiyar Abin da Ya Jawo Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Shigo da Indomie a Yau

Gaskiyar Abin da Ya Jawo Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Shigo da Indomie a Yau

  • Jita-jita tayi yawa a game da cewa ana samun sinadarin Ethylene oxide a cikin taliyar Indomie
  • Shugabar Hukumar NAFDAC ta kasa ta jaddada haramcin shigo da Indomie yayin da za ayi gwaji
  • A makon nan aka ji Farfesa Mojisola Adeyeye tana bada sanarwar binciken abin da ke cikin taliyar

Abuja - Hukumar NAFDAC mai kula da abinci da magunguna a Najeriya ta hana a shigo da taliyar Indomie cikin kasar nan har sai an yi bincike.

Jaridar Vanguard ta ce Shugabar NAFDAC ta kasa, Farfesa Mojisola Adeyeye ta shaida haka a sa’ilin da ta tattauna da 'yan jarida a ranar Litinin.

Da ta ke magana a garin Abuja, Mojisola Adeyeyeta ce NAFDAC ta dauki matakin ne bayan ana ta rade-radin taliyar tana dauke da ethylene oxide.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Shafuka 90 a Kan Jerin Nasarorin da Buhari Ya Samu

Masana kimiyya da lafiya sun ce sinadarin yana iya jawo cutar kansa a jikin ‘Dan Adam.

Farfesa Adeyeye ta ce tuni har bangaren kula da binciken abinci na hukumar NAFDAC ya fara shirin gudanar da bincike a kan taliyar Indomie.

Indomie
Kwalayen Indomie Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin Shugabar Hukumar NAFDAC

“An haramta shigo da Indomie cikin kasar nan na tsawon shekara da shekaru, ta na cikin jerin abincin da gwamnati ta hana shigo da su.
Ba a yarda a rika shigo da ita Najeriya ba, a dalilin haka Indomie ba ta da rajista da NAFDAC.
Abin da mu ke yi kara hattara ne domin tabbatar da cewa ba a shigo da shi a boye ba, idan an nemi ayi hakan, kayan aikinmu za su gano shi.
Mu na kuma so mu tabbata an yi gwaji a kan kayan kanshin da ake amfani da su wajen dafa indomie da sauran kananan taliya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Tattago Binciken Sanatan da Ake So Ya Zama Shugaban Majalisa

Wanan shi ne abin da bangarorin hukumar NAFDAC na FSAN da PMS su ke yi a makon nan wajen hada taliyar da kuma cikin kasuwanni.

- Farfesa Mojisola Adeyeye

An fara shirin bincike

The Cable ta ce shugabar ta NAFDAC tayi alkawarin za a rika sanar da ‘Yan Najeriya halin da ake ciki a game da abin da aka gano wajen binciken.

Daga yau Talata, za a fara binciken sinadaran da ke cikin Indomie, amma kamfanin da ke hada taliyar na Indofood ya musanya zargin da ake yi masa.

Ma'aikata za su sha wahala

A rahoton da mu ka fitar, an ji Godwin Obaseki ya ce ikon Allah kurum zai sa gwamnatin tarayya da na jihohi su iya biyan albashi bayan Yunin 2023.

Gwamnan Jihar Edo yana ganin dole a koma buga kudi ko a cire tallafin fetur nan da ‘yan kwanaki, ya ce duk wanda aka yi zai kara jefa al’umma a kunci.

Kara karanta wannan

To fah: Wani sabon maganin tari ya shigo Najeriya, NAFDAC ta yi gargadin yana kisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel