Hukumar EFCC Ta Tattago Binciken Sanatan da Ake So Ya Zama Shugaban Majalisa

Hukumar EFCC Ta Tattago Binciken Sanatan da Ake So Ya Zama Shugaban Majalisa

  • EFCC ta aikawa Sanata Godswill Akpabio takarda, ta ce ya kai kan shi gabanta a watan Mayu
  • An yi hakan ne lokacin da ‘Dan siyasar yake harin shugabancin majalisar dattawan Najeriya
  • Akpabio ya yi Gwamna sau biyu a Akwa Ibom, kuma ya rike Ministan Neja-Delta a mulkin APC

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta bukaci Godswill Akpabio ya mika kan shi a hedikwatarta domin a iya yin bincike a kan shi.

A rahoton da muka samu daga Premium Times, an ji Sanata Godswill Akpabio zai amsa tambayoyi a kan zargin rashin gakiya da EFCC ta ke yi masa.

Hukumar EFCC ta bukaci Sanata Akpabio ya mika kan shi da kan shi a ranar 9 ga Mayu.

Sahara Reporters ta ce tsohon Ministan harkokin Neja Delta yana cikin manyan masu neman zama shugaban majalisar dattawa a karkashin APC.

Kara karanta wannan

Jirgin saman NigeriaAir Zai Fara Tashi Kafin Shugaba Buhari Ya Bar Aso Rock – Minista

Wannan umarni ya na cikin wata wasika da hukumar ta aikawa tsohon Gwamnan na Akwa Ibom ta hannun Lauyansa, Umeh Kalu, SAN a Afrilun nan.

Godswill Akpabio bai da lafiya?

Da aka rubutawa Akpabio takarda irin haka a watan Maris, sai ya maida amsa ta bakin Lauyansa da ba zai samu zuwa ba domin zai je asibitin kasar waje.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akpabio
Akpabio da su Shugaba Buhari Hoto: thebridgenewsng.com
Asali: UGC

Punch ta ce Umeh Kalu, SAN ya ba EFCC uzurin cewa wanda yake karewa yana fama da ciwon sanyi na Pneumonia da kuma larurar zuciya ta arrhythmia.

Masana sun ce arrhythmia tana jawo zuciyar mutum ta rika bugawa ba daidai ba, ganin haka likitoci su ka ba shi shawara ya nemi magani a ketare.

Magana ta tashi!

Rashin lafiyar ta jawo Kalu ya roki jami’an EFCC su dakatar da gayyatar sai bayan hutun azumi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Babu mamaki za a binciki ‘dan siyasar ne a kan rawar da ya taka a lokacin yana Gwamnan Akwa Ibom na shekaru takwas a PDP ko da ya zama Minista.

Bayan an aiko da sabuwar gayyatar, Premium Times ta tuntubi Mai magana da yawun bakin Akpabio, Jackson Udom wanda ya nuna bai san an yi ba.

Mukamai a gwamnatin Tinubu

An ji labari Mai magana da bakin Atiku Abubakar ya ce Nasir El-Rufai zai zama SGF, Babatunde Fashola zai rike mukamin AGF a gwamnatin Bola Tinubu.

A karambaninsa, Daniel Bwala ya ce daga cikin Ministocin gobe akwai James Faleke, Ben Ayade, Tukur Buratai, Femi Fani Kayode, da Nyesom Wike

Asali: Legit.ng

Online view pixel